in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan sabbin tamburan kirar kaya a kasar Sin a shekarar 2018 ya kai miliyan 1.602
2019-01-08 14:40:24 cri

Darektan hukumar dake kula da 'yancin mallakar tambarin kirar kaya ta kasar Sin, Shen Changyu, ya ce yawan sabbin tamburan kirar kaya da Sinawa suka yi a bara ya kai miliyan 1 da dubu 602, adadin da ya karu da kashi 18.1% bisa na shekarar 2017.

Mr. Shen Changyu ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a nan birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin. Yana mai cewa, kasar Sin za ta kara kokarin kare 'yancin mallakar tambarin kirar kaya a bana. Kaza lika kasar za ta tsara cikakken shirin raya harkar kare 'yancin mallakar tambarin kirar kaya, da bullo da manufofi masu alaka da aikin, gami da shirin kafa wata cibiyar aikin kare 'yancin mallakar kira. A sa'i daya kuma, kasar za ta zurfafa hadin gwiwarta da sauran kasashe a wannan fanni, in ji jami'in. Sannan Mr. Shen Changyu ya bayyana cewa, a shekarar 2018, karfin samar da sabon tambarin kirar kaya a kasar Sin ya kai wani sabon matsayi. Yana mai cewa, "Yawan sabbin tamburan kirar kaya da Sinawa suka yi a bara ya kai miliyan 1 da dubu 602, adadin da ya karu da kashi 18.1 cikin dari bisa na shekarar 2017. Yawan sabbin tamburan kirar kaya tsakanin Sinawa dubu goma ya kai 11.5. Bugu da kari, yawan takardun neman samun amincewar sabbin tamburan kirar kaya da sauran kasashen duniya suka gabatar domin neman amincewa a kasar Sin bisa 'yarjejeniyar yin hadin gwiwa a fannonin kare 'yancin mallakar fasaha ya kai dubu 55 a shekarar 2018, wato ya karu da kashi 9 cikin dari bisa makamancin lokacin shekarar 2017."

Sannan Mr. Shen Changyu ya bayyana cewa, a shekarar 2019, kasar Sin za ta kara mai da hankali wajen kare 'yancin mallakar fasaha. Ya ce, kasar Sin za ta kara mai da hankali wajen inganta dokokin da suke shafar aikin kare 'yancin mallakar fasaha da sabbin fasahohin zamani da aka samu a wasu sabbin fannoni bisa ci gaban zamani, ta yadda za ta tsara da kuma fitar da shirin kare 'yancin mallakar fasaha daga dukkan fannoni, tare da kafa tsarin aiwatar da su. A waje daya kuma, hukumar kare hakkin mallakar fasaha ta kasar Sin za ta tsara manufofi da kuma matakai na karfafa aikin kare 'yancin mallkar fasaha. Dadin dadawa, Mr. Shen ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya a fannin kare 'yancin mallakar fasaha.

"Za a tabbatar da ganin an aiwatar da manufofin kare 'yancin mallakar fasaha da aka tsara a yayin taron manyan jami'an kasa da kasa da shawarar 'ziri daya da hanya daya' ta shafa. Sannan za a ci gaba da yada ka'idodin kasa da kasa na yin rajistar tambarin kayayyaki na Madrid da yarjejeniyar yin hadin gwiwar kare 'yancin mallakar fasaha tsakanin kasa da kasa."

Mr. Shen Changyu ya kuma jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da ingiza ganin an bullo da ka'idojin kare 'yancin mallakar fasaha da suka dace bisa ka'idodjin daidaito da kuma amincewa da juna. Tabbas za ta tsaya wa matakan daidaita harkokin kasa da kasa bisa ra'yoyin bangarori da dama, da kuma daidaita matsalolin da za su fito a fannin kare 'yancin mallakar fasaha, sannan za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kungiyar kare 'yancin mallakar fasaha ta kasa da kasa da taka muhimmiyar rawa wajen tsara da kuma gyara ka'idodjin kare 'yancin mallakar fasaha.

"Tabbas za mu ci gaba da daga tutarmu ta yin hadin gwiwa, da kuma karfafa yin hadin gwiwar aikin kare 'yancin mallakar fasaha da shawarar ziri daya da hanya daya ta shafa. Hukumomin kare 'yancin mallakar fasaha na kasashen Sin da Amurka da Turai da Japan da kuma na Koriya ta kudu za su kara yin hadin gwiwa, kuma za a kara yin hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICKS da sauran bangarori. Bugu kari, za ta kara yin hadin gwiwa tsakanin bangarori biyu, wato tsakanin Sin da wata kasa daban." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China