in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangaren aikewa da sakonni na kasar Sin ya bukasa cikin sauri a shekarar 2018
2019-01-07 11:12:39 cri
Kamfanonin aikewa da sakonni na kasar Sin sun yi jigilar kayayyaki kimanin biliyan 50.5 a shekarar 2018, inda aka samu karuwar kashi 25.8 bisa 100 a makamacin lokacin bara, kamar yadda alkaluman da hukumar kula da ayyukan aikewa da sakonni ta kasar Sin (SPB) ta fitar.

Bangaren aikewa da sakonnin yana tallafawa ayyukan ciniki ta intanet a duk shekara da kusan yuan triliyan 6.9 da kuma ciniki ta intanet dake tsallaka kan iyakoki na sama da yuan biliyan 350 yayin da ya samar da sabbin guraben ayyukan yi sama da 200,000 a 2018.

"Ana aikewa da sakonni kimanin biliyan 100 a fadin duniya a duk shekara. Kasar Sin tana daukar kashi 50 bisa 100 na adadin sakonnin," in ji Ma Junsheng, shugaba hukumar SPB.

A yankunan karkara, kashi 92.4 bisa 100 na garuruwa suna amfana da ayyukan aikewa da sakonnin cikin gaggawa, inji Ma.

Kimanin sakonni biliyan 12 ne aka aika su zuwa yankunan karkara a shekarar da ta gabata, wadanda aka yi jigilar kayayyakin da darajarsu ta kai sama da yuan biliyan 700 a tsakanin birane da yankunan karkara.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China