in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya yi tsokaci kan sakamakon taron kolin Beijing na FOCAC a fannoni 6
2019-01-07 10:55:06 cri

Jiya 6 ga wata, agogon kasar Senegal, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya gana da manema labarai tare da takwaran aikinsa na kasar ta Senegal Sidiki Kaba a Dakal, fadar mulkin kasar bayan shawarwarin da suka yi tsakaninsu, inda ya yi tsokaci kan kokarin da kasashen biyu wato Sin da Senegal suka yi domin aiwatar da sakamakon da aka samu yayin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da aka shirya a birnin Beijing na kasar Sin daga fannoni shida.  

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya bayyana cewa, taron kolin Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da aka gudanar a shekarar 2018 ya samu cikakkiyar nasara, ko shakka babu yana da babbar ma'ana a tarihin raya huldar Sin da Afirka, haka kuma zai kasance abin koyi ga huldar hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Afirka da sauran kasashen duniya.

Jami'in ya kara da cewa, abu mafi jawo hankalin al'ummomin kasashen duniya shi ne sassan biyu wato Sin da Afirka sun fi mai da hankali kan saurin gudanar da aiki yayin da suke yin hadin gwiwa a fannoni daban daban, misali bayan kammalar taron, nan take hukumar kula da aiki ta kasar Sin ta fara gudanar da aikinta bisa matakai daban daban, ta hanyar yin shawarwari da kasashen Afirka, nan gaba kuma kasar Sin za ta kara karfafa cudanya tsakaninta da kasashen Afirka, musamman ma da kasar ta Senegal wadda ita ce kasar dake jagorantar taron kolin Beijing tare da kasar Sin a fannoni shida:

Na farko, ya dace a gina kyakkyawar makomar Sin da Afirka, a halin da ake ciki yanzu, kasashen duniya suna fama da yanayin rashin daidaito, lamarin da ya kawo barazana ga dokokin kasashen duniya da tsarin gudanar da harkokin cinikayya tsakanin bangarori da dama, tarin kasashe masu tasowa su ma ba su tsira ba, kamar yadda aka sani, kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, haka kuma yawancin kasashen Afirka su ma kasashe ne masu tasowa, a don haka wajibi ne kasar Sin da kasashen Afirka su hada kai tare domin gina kyakkyawar makomarsu, ta yadda za su murkushe makarkashiyar hana ci gabansu, tare kuma da kiyaye 'yanci da muradunsu.

Na biyu, ingiza hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu wajen aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya da kuma cimma burin muradun raya kasashen Afirka nan da shekarar 2063 na kungiyar tarayyar Afirka wato AU. Kawo yanzu kasashen Afirka da yawansu ya kai 37 da kungiyar AU sun riga sun shiga shawarar ziri daya da hanya daya, kasar Sin tana son hada kai tare da aminan kasashen Afirka domin samar da karin damammakin hadin gwiwa dake tsakaninsu.

Na uku, kasar Sin za ta tsara matakan da suka dace bisa hakikanin yanayin da ko wace kasar Afirka ke ciki, yayin da ake kokarin aiwatar da sakamakon taron kolin Beijing, hakika yanayin da kasashen Afirka suke ciki ya sha bamban da juna, a don haka ya dace a tsara shiri bisa bukatunsu a fannonin samar da taimako da rancen kudi da zuba jari da sauransu.

Na hudu, sa kaimi kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka ta hanyar yin kirkire-kirkire domin samun sakamako mai gansarwa. Kasar Sin tana fatan kamfanonin kasar za su kara zuba jari kai tsaye a kasashen Afirka, haka kuma tana goyon bayansu da su gudanar da harkokinsu a kasashen nahiyar, ta yadda za a cimma burin kyautata kayayyakin more rayuwar jama'ar kasashen, tare kuma da bunkasa hadin gwiwa dake tsakanin sassan biyu a fannonin kimiyya da fasaha irin na zamani, ta yadda za su gudanar da hadin gwiwa mai inganci tsakaninsu lami lafiya.

Na biyar, za a yi kokari domin al'ummomin kasar Sin da kasashen Afirka su ci gajiyar sakamakon da aka samu yayin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka na Beijing, har kullum, ana mai da hankali matuka kan moriyar al'umma yayin da sassan biyu suke gudanar da hadin gwiwa, a don haka matakai guda takwas da za su dauka za su taka rawa wajen yaki da talauci da samar da karin guraben aikin yi da kyautata rayuwar al'umma a kasashen Afirka.

Na shida, za a yi kokarin ganin sauran kasashen duniya sun gudanar da hadin gwiwa da kasashen Afirka, an kammala taron kolin Beijing cikin nasara, lamarin da ya jawo hankalin kasashen duniya matuka, haka kuma za su kara mai da hankali kan ci gaban kasashen Afirka, muna fatan za su kara zuba jari a nahiyar, tare kuma da gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu da kasashen Afirka. A ko da yaushe kasar Sin tana nacewa ga manufar gudanar da hadin gwiwa da kasashen Afirka ba tare da wata rufa rufa ba, ya kamata a girmama muradun ci gaban Afirka, kuma ya kamata a mayar da nahiyar Afirka a matsayin babban dandalin hadin gwiwar kasa da kasa, amma ba dandalin takara na manyan kasashe ba.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China