in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Na'urar binciken duniyar wata ta Sin ta sauka a sashe mafi nisa na duniyar wata
2019-01-04 12:28:43 cri

A karon farko na'urar binciken duniyar wata ta Sin samfurin Yutu-2 ko Jade Rabbit-2, ta sauka a sashe mafi nisa na duniyar wata. Na'urar ta sauka a yankin na wata mafi nisa ne da karfe 10:22 na daren jiya Alhamis, bayan ta rabu da kumbon dake dauke da ita.

Hukumar dake lura da binciken sararin samaniya ta kasar Sin CNSA ta sanar da cewa, an nadi saukar na'urar, da kyamarar daukar hotuna dake aikowa da sakwanni kai tsaye zuwa duniyar bil'adama, ta tauraron dan Adam na "Queqiao".(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China