in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yaki Da Boko Haram: Goyon Bayanmu Sojoji Ke Bukata –Gwamna Shettima
2019-01-03 16:29:10 cri
Gwamna Kashim Shettima, na Jihar Borno, ya yi kira da a bayar da cikakken hadin kai da goyon baya domin karfafa gwiwar dakarun kasar nan wajen samun nasarar yakin da suke fafatawa da 'yan ta'addan Boko Haram.
Shettima, ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake halartar wani mahimmin taro na Jami'an tsaro wanda aka shiryawa masu ruwa da tsaki a ranar Litinin da dare a Maiduguri.

Kamfanin dillancin labarai na kasa, ya kawo rahoton cewa, Shettima tare da sauran mahalarta taron, sun yi wata ganawa ta sirri da tsakiyar daren, domin samar da mafita a kan sake bayyanar ayyukan 'yan ta'addan na Boko Haram, da suke ta kai hare-hare a sassan Jihar ta Borno.

Shettima, ya yi kira ga al'umma da su hada kai ba tare da nuna bambanci ba, domin goyawa Sojojin Nijeriya, 'yan sanda, da sauran jami'an tsaro baya, domin cimma nasarar kawo karshen 'yan ta'addan na Boko Haram, da maido da zaman lafiya a Jihar.
Ya ce, "Batun gaskiya shi ne, a lokacin da zaratan Sojojinmu suka sami nasarori masu yawa, a yau kuma muna sake fuskantar kalubale masu girma a Jihar ta Borno, wadannan kalubalen kamata ya yi su karfafa mana imanin mu wajen ci gaba da goyon bayan dakarun Sojinmu, 'Yan sanda, Jami'an tsaro na DSS, mayakan sa kai na farin kaya, da sauran hukumomin siyasa na tarayya, domin kawo karshen ta'addancin 'yan kungiyar ta Boko Haram.

"Na sadu da Shugaban kasa sau da yawa, hatta ma a 'yan kwanakin nan na sadu da shi. Na kuma jagoranci 'yan majalisun Jiharmu zuwa ga Shugaban kasan, a kuma dukkanin tattaunawar namu, kowa ya shaida cewa, Shugaban kasan da gaske yake yi a bisa yanda ya nuna damuwarsa a kan halin da al'umman na sashen arewa maso gabas suke ciki.

"Wannan yakin namu ne baki-daya, duk muna da alhakin tabbatar da maido da zaman lafiya a Jihar Borno, wannan ne kuma dalilin da ya sanya muka yanke shawarar kiran wannan taron a kan tsaro, a inda muka gayyato mutane na musamman.
Shettima, ya yi nuni da cewa, mahalarta taron za su tattauna ne a kan halin da ake ciki, sai kuma su kawo shawarwarin da za a kaiwa Shugaban kasa.

Ya ce gwamnatin Jihar ta aiwatar da wasu mahimman ayyuka domin sake ginin Jihar, farfadowa da sake zaunar da al'umman Jihar a wuraren su na asali. A cewar sa, sun gina sama da gidajen zama 30,000, makarantu, Asibitoci, wuraren shan ruwa, kasuwanni, cibiyoyin tsaro, wuraren ibada, da makamantan su, domin tallafawa kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na magance matsalolin da ayyukan 'yan ta'addan ya haifar.

Kamfanin dillancin labaran ya kawo rahoton cewa, shugabanni daga sassan hukumomin tsaro, Sarakunan gargajiya, Dattawan Jihar, Sanatocin Jihar, Da wakilan Majalisun tarayya da na Jihar duk sun halarci taron.

Sauran mahalarta taron sun hada da, wasu Shugabannin kananan hukumomi da aka zabo, Kwamishinoni, Shugabannin Jami'ar Maiduguri, da wasu shugabannin manyan makarantun Jihar da aka zabo, wakilai daga kungiyar kwadago ta kasa, NLC, kungiyar Lauyoyi ta kasa, kungiyar manema labarai shugabannin kungiyoyin mata. (Daga Leadership A Yau)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China