181228-Yadda-baki-ke-kallon-manufar-yin-gyare-gyare-da-bude-kofa-ta-kasar-Sin-luba.m4a
|
Daga ranar 18 zuwa 22 ga watan Disamban shekarar 1978, an gudanar da cikakken zama na uku na kwamitin koli na 11 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, taron da aka dauka a matsayin mafari na fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a kasar ta Sin. A cikin wadannan shekaru 40 da suka wuce, manufar ta kawo gagaruman nasarori a kasar, nasarorin da suka hada da fid da mutane miliyan 700 daga kangin talauci da kuma mai da kasar zama ta biyu a duniya ta fannin ci gaban tattalin arziki. A sa'i daya kuma, manufar ta kara samun yabo da amincewar kasashen duniya.