in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga waje da kasar Sin ta aiwatar ta taimakawa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka
2018-12-27 13:18:59 cri

Shekarar 2018 shekara ce ta cika shekaru 40 da kasar Sin ta kaddamar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga waje, kuma shekara ce da ake karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. A kwanan baya, a lokacin da yake tabo wannan manufar da kasar Sin ta dauka, malam Hussein Ismail, mai nazarin harkokin siyasa na hukumar kula da aikin jarida ta Masar, wanda ya kware sosai kan batun kasar Sin ya bayyana cewa, hadin gwiwar da ake yi tsakanin Sin da Afirka ta samu ci gaba ne sakamakon wannan manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga waje, har ma ta taimakawa kara ci gaban wannan hadin gwiwa.

Malam Hussein Ismail ya shafe kusan shekaru 20 yana zama da kuma yin aiki a kasar Sin tun daga shekarar 1992. Da idonsa ne ya ga yadda kasar Sin ta samu ci gaba cikin sauri matuka a cikin shekaru 40 bayan da kasar ta kaddamar da manufar yin gyare-gyare da bude kofarta ga waje. A lokacin da yake bayyana mamakinsa ga babban ci gaban da kasar Sin ta samu, ya kuma lura cewa, bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga waje, kasar Sin ta kuma habaka matakanta na fita waje, har ma ta samar da dimbin kyawawan dabarun neman ci gaba ga kasashen Afirka. Malam Hussein Ismail yana mai cewa, "Yanzu wasu kasashen Afirka, kamar kasarmu Masar suna cikin lokaci na yin gyare-gyare, ayyukan yin gyare-gyare da bude kofa ga waje da kasar Sin ta yi cikin shekaru 40 da suka gabata, sun kasance kamar misalai ne gare mu. A 'yan shekarun nan, bisa taimakon kasar Sin, an samar da dimbin ayyukan more rayuwar al'umma a Afirka. A lokacin da kasar Sin take ci gaban kanta, tana samar da wani salon neman ci gaba mai amfani ga wasu kasashen Afirka wadanda suke son yin hadin gwiwa, ta yadda za su iya kubutar da kansu daga mawuyacin hali da kuma tabbatar da kwanciyar hankalin zaman al'umma."

A cikin jawabin da ya bayar a gun babban taron murnar cika shekaru 40 da kaddamar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga waje da aka shirya kwanan baya, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ce, dole ne a tsaya kan "fannoni 9". Daga cikinsu, ra'ayinsa na "dole ne a tsaya kan matsayin habaka kara bude kofa, ta yadda za a iya kafa wata al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama" ya burge Hussein Ismail sosai. Malam Hussein Ismail ya bayyana cewa, bayan da ta kaddamar da manufar yin gyare-gyare da bude kofarta ga waje, shawarar bunkasa "Ziri daya da hanya daya" da kuma "shirin yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a fannoni 10" da kasar Sin ta bayar sun samar da dimbin kayayyakin more rayuwar al'umma da kasashen Afirka suke bukata cikin gaggawa. A halin da ake ciki mai sarkakiya a duk fadin duniya, wasu kasashen Afirka na fuskantar matsaloli a lokacin da suke kokarin neman ci gaba, amma ko shakka babu, ra'ayin "kafa wata al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama" amsa ce mafi dacewa ga matsalolin da suke fuskanta. "A lokacin da kasar Sin take yin gyare-gyare da bude kofarta ga waje, tana kuma kokarin sauke nauyin kasa da kasa da aka dora mata. Kasar Sin ta gabatar da wasu shawarwarin neman ci gaban duk duniya. A cikin wadannan shawarwari, dukkan kasashen duniya zasu iya more sakamakon da suka samu, su yi hadin gwiwa wajen shimfida zaman lafiya da kawar da rikice-rikicen shiyya-shiyya, da kokarin tabbatar da kwanciyar hankali da kuma kafa dangantakar hadin gwiwa irin ta sada zumunta tsakanin kasa da kasa tare, sune shawarwarin da kasar Sin ta gabatar da suka fi jawo hankulan gamayyar kasa da kasa."

Malam Hussein Ismail ya kuma nuna cewa, bisa manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga waje ta kasar Sin, ana hanzarta bunkasa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. Kasar Masar kasa ce dake da yawan al'umma mafi yawa na biyu a Afirka, tana yankin dake iya hada Afirka, da Turai da kuma Asiya. Sabo da haka, tana taka muhimmiyar rawa wajen daidaita harkokin neman ci gaba tare. Yana fatan kasashen Sin da Masar zasu iya kara yin mu'amala da hadin gwiwa domin bayar da sabuwar gudummawa ga hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka.

"Kasar Masar tana da dimbin fasahohin yin hadin gwiwa da sauran kasashen Afirka. Kasar Sin tana da karfi da kuma fata na yin hadin gwiwa damu Afirka domin bunkasar Afirka. Ina da imani cewa, kasashen Sin da Masar zasu iya sauke nauyin dake bisa wuyansu da yin kokari tare bisa ka'idodin yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, ta yadda zasu iya cin moriya da nasara tare da sauran kasashen Afirka." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China