in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na maraba da musaya a fannin tsaro da Japan
2018-12-26 21:22:35 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce tsarin hadin gwiwa tsakanin Sin da Japan a bangaren tsaron teku, da tsaron sararin samaniya na da matukar muhimmanci, kuma zai taimakawa wajen kaucewa sabani, da rashin fahimtar juna tsakanin sassan biyu.

Uwar gida Hua ta bayyana hakan ne a yau Laraba, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa a nan birnin Beijing.

Hua Chunying na amsa tambaya ne game da taron shekara shekara irin sa na farko da kasashen biyu suka kira a wannan fanni na tsaro, wanda ya gudana tsakanin ranekun 26 zuwa 27 ga watan Disambar nan a Beijing.

Kasashen biyu sun sanya hannu kan takardar fahimtar juna, game da kafa wani tsarin musamman da ya shafi hadin gwiwar tsaro, yayin ziyarar da firaminstan kasar Sin Li Keqiang ya kai Japan a watan Mayun da ya shude.

Hua ta ce kaddamar da wannan manufa na da ma'anar gaske ga hukumomin tsaron kasashen biyu, wajen bunkasa fahimtar juna, da karfafa amincewa juna, da kaucewa sabani da rashin fahimta, ko yiwa juna fahimta bisa kuskure. Baya ga wanzar da zaman lafiya da daidaito tsakanin kasashen, da manufar ka iya haifarwa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China