Rahotanni daga jami'an hukumar kasar dake lura da bala'u na cewa, yawan mutane da suka rasa rayukan su, sakamakon wannan ibtila'i ta kai sama da mutum 20,000.
Da yaka tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Larabar nan, mai magana da yawun hukumar Sutopo Purwo Nugroho, ya ce Tsunamin ta raba mutane 21,921 dake yankunan bakin teku da gidajen su, adadin da ya haura 16,082 da aka kididdige a ranar Talata.