181225-sharhi-Sanusi.m4a
|
A yayin taron da kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya shirya a kwanan baya game da ayyukan tattalin arziki da za a yi a shekara mai kamawa, an tabbatar da cewa, dole ne a yi kokarin rigakafi da kuma kawar da haddura masu tsanani dake kasancewa a fannin hada-hadar kudi, ta yadda za a iya daidaita shirye-shiryen hada-hadar kudi kamar yadda ya kamata a shekarar 2019 domin samar da karin taimako ga tattalin arziki. A cikin shekaru 40 da aka kaddamar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofar kasar Sin ga ketare, sana'o'in bankuna da kamfanonin inshora na kasar Sin sun samu ci gaba sosai. Mr. Liang Tao, mataimakin shugaban kwamitin sa ido kan bankuna da kamfanonin inshora na kasar Sin ya bayyana cewa, "Kawo yanzu, jimillar kaddarorin da bankunan kasar Sin suke da su ya kai RMB yuan biliyan dubu 260, wato tana sahun gaba a duk duniya. Bankuna fiye da 130 na kasar Sin sun shiga jerin bankuna mafiya girma dubu 1 a duk fadin duniya. Daga cikinsu, bankuna 4 mafi girma a kasar Sin sun zama muhimman bankuna da suka kafa sassansu a duk fadin duniya. Sannan jimillar kaddarorin da kamfanonin inshora na kasar Sin suke da shi ya kai RMB yuan biliyan dubu 18. Sakamakon haka, yanzu kasar Sin ta zama kasuwar inshora mafi girma ta biyu a duk duniya."
Liang Tao ya kuma bayyana cewa, a 'yan shekarun baya, bankuna da kamfanonin inshora na kasar sin sun fi maida hankali wajen daidaita harkokinsu bisa doka da kuma taimakawa masana'antu. Bisa hakikanin halin da ake ciki yanzu, bankuna da kamfanonin inshora na kasar Sin na samun ci gaba kamar yadda ake fata, ana kuma sarrafa hadduran dake kasancewa a fannin hada-hadar kudi.
"A cikin watanni 11 da suka gabata na bana, bankunan kasar Sin sun samar da karin rance RMB yuan biliyan dubu 14.8 ga masana'antu, wato ya karu da RMB yuan biliyan dubu 1.5. Sannan kamfanonin inshora sun samar da inshora ga sassa daban daban na al'ummomin kasar Sin da darajarsu ta kai kudin RMB yuan trilian 6165."
A yayin taron da kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya shirya a kwanan baya game da ayyukan tattalin arziki da za a yi a shekara mai kamawa, an tabbatar da cewa, dole ne a yi kokarin rigakafi da kuma kawar da haddura masu tsanani dake kasancewa a fannin hada-hadar kudi, ta yadda za a iya daidaita shirye-shiryen hada-hadar kudi kamar yadda ya kamata a shekarar 2019 domin samar da karin taimako ga tattalin arziki. Mr. Han Wenxiu, mataimakin direktan ofishin kwamitin kula da harkokin tattalin arziki da hada-hadar kudi na kwamitin kolin JKS yana ganin cewa, "Ya kamata a daidaita manufofin kudi bisa sauyin halin da ake ciki kamar yadda ake fata, ta yadda za a iya tabbatar da samar da isassun kudade a kasuwa. Musamman dole ne a yi kokarin kawar da matsalolin da kamfanoni masu zaman kansu da kananan kamfanoni suke fuskanta wajen samun rance daga bankuna. Ya kamata a yi kokarin kafa wasu bankuna masu zaman kansu da bankunan dake iya bada taimako ga unguwannin da suke ciki. Sannan a yi kokarin sa kaimi ga bankunan kasuwanci da bankunan raya kasuwanci a yankunan karkara da asusun bada lamuni a yankunan karkara da su yi aikinsu kamar yadda aka tabbatar musu a lokacin kafuwarsu."
Yanzu, koda yake wasu kamfanoni masu zaman kansu da kananan kamfanoni sun kashe kudi da yawa wajen neman samun rance daga bunkuna, amma daga karshe dai ba su iya samu ba. Wannan ya zama wata matsalar da ke jawo hankulan zaman al'ummar kasar Sin. Game da matsalar, Mr. Liang Tao ya ce, a lokacin da ake tabbatar da rage faruwar hadaruka a fannin hada-hadar kudi, kwamitin sa ido kan harkokin bankuna da kamfanin inshora na kasar Sin ya riga ya nemi bankuna da kamfanonin inshora da su kara bada rance ga kamfanoni masu zaman kansu da wasu kananan kamfanoni, ta yadda za su iya hanzarta warware matsalolin da suke fuskanta.
A yayin taron da kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya shirya a kwanan baya game da ayyukan tattalin arziki da za a yi a shekara mai kamawa, an kuma sanya aikin kara bude kofar kasar Sin ga ketare daga dukkan fannoni a sahun gaba da za a yi shekara mai kamawa. Mr. Liang Tao ya bayyana cewa, kwamitinsa ya riga ya fitar da matakai 15 na bude kofar bankuna da kamfanonin inshora na kasar Sin ga ketare. Mr. Liang yana mai cewa, "Kawo yanzu, wasu bankuna da kamfanonin inshora na jarin waje sun riga sun samu izinin shiga kasuwannin kasar Sin. A nan gaba, a lokacin da muke inganta aikin rigakafi da tinkarar hadduran hada-hadar kudi, za mu hanzarta aiwatar da matakan da muka fitar domin tabbatar da inganta ayyukan bude kofarmu ga ketare." (Sanusi Chen)