A makon jiya, kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya shirya wani taron, inda aka takaita ayyukan tattalin arziki da aka yi a shekarar 2018, da kuma nazarta halin tattalin arziki da ake ciki a kasar Sin, sannan aka fitar da shirye-shirye da ka'idoji kan yadda za a bunkasa tattalin arzikin kasar Sin a shekara mai kamawa. Bisa bayanan da aka fitar a yayin taron, idan ana son sanin yadda ake bunkasa tattalin arzikin kasar Sin, ya kamata a yi nazari daga fannoni 3.
Da farko dai, dole ne a kara sanin ka'idodji 5, ta yadda za a iya sanin yadda ake namijin kokarin neman ci gaban tattalin arzikin kasar Sin.
Shekarar 2018 tana da muhimmanci sosai ga kasar Sin. A wannan shekara, wasu sun fara nuna adawa da kokarin bunkasa tattalin arzikin duk duniya na bai daya, sannan takaddamar cinikayya da ake yi ta tsananta, halin da ake ciki a wajen kasar Sin ba shi da tabbaci, har ma gamayyar kasa da kasa ta fi maida hankali kan yadda kasar Sin za ta kara yin gyare-gyare da bude kofarta ga ketare a cikin farkon shekara domin cimma burin da aka kafa a yayin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19. A yayin wannan taron da aka yi a makon jiya, an bayar da wasu misalai, kamar yadda kasar Sin ta kan daidaita matakan bunkasa tattalin arziki daga dukkan fannoni bisa sauyin yanayin da ake ciki, da kuma kokarin yin gwagwarmayar yaki da kalubaloli masu tsanani, da kawar da kangin talauci da matsalolin gurbata muhalli da kuma yadda ta yi kokarin inganta rayuwar al'umma. An yi tsammanin cewa, "kasar Sin ta samu sabon ci gaba wajen cimma burin kafa zaman al'umma mai matsakaicin karfi daga dukkan fannoni sakamakon bunkasar tattalin arzikin kasar ba tare da tangarda ba kamar yadda ake fata, da bada tabbaci ga zaman al'ummar kasar a shekarar bana. An sha fama da dimbin wahaloli domin kokarin samun kyakkyawan sakamako." Wannan ya alamta cewa, kwamitin kolin JKS ya bada tabbaci sosai ga sakamakon da aka samu wajen bunkasar tattalin arzikin kasar Sin, ya kuma bayyana kwarewa mai inganci sosai na shugabannin kasar Sin wajen daidaita matsaloli masu sarkakiya, da kuma karfin tinkarar hadduran da tattalin arzikin kasar Sin yake da shi.
Yayin taron, an yi nuni da cewa, bayan kokarin da kasar Sin ta yi a cikin shekara guda da ta gabata, ta kara zurfafa fahimtarta kan fannoni biyar na aikin tattalin arzikinta a sabon yanayin da ake ciki yanzu, wato dole ne a nacewa jagorancin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, dole ne a kara fahimtar yanayin da ake ciki yanzu bisa hangen nesa, dole ne a sarrafa yanayin da ake ciki bisa manyan tsare-tsare, dole ne a maida hankali kan ra'ayin jama'a, haka kuma dole ne a kara kwarin gwiwa ga zuciyar bangarori daban daban a fadin kasar domin su kara sanya kokari kan aikinsu, a cikin wadannan fannoni biyar, na farko da na biyu sun fi muhimmanci. Bisa matsayinta na babbar kasa mafi karfin tattalin arziki ta biyu a duniya, da kuma matsayinta na kasa mafi girma wajen cinikayya a fadin duniya, karfin jagorancin aikin tattalin arziki yana da muhimmanci matuka, a sa'i daya kuma, kila ne za a gamu da matsala yayin da ake kokarin raya tattalin arziki a kasar, a don haka dole ne a sarrafa yanayin tattalin arzikin kasar bisa manyan tsare-tsare, ta yadda za a cimma burin ci gaban tattalin arziki mai inganci yadda ya kamata.
Na biyu, kasar Sin za ta ci gaba da samun bunkasuwa cikin sauri.
A shekarar 2018 da ake ciki, an gamu da takaddamar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen Sin da Amurka, sai dai an nuna shakku cewa, kila ne tattalin arzikin kasar Sin ba zai iya samun ci gaba cikin sauri ba, game da wannan, a taron raya tattalin arzikin kasar Sin na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin an bayyana cewa, yanzu tattalin arzikin kasar Sin yana gudana yadda ya kamata, duk da cewa, ya gamu da matsala, kana an jaddada cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai samu ci gaba cikin sauri kamar yadda take yanzu.
Dalilin da ya sa aka yi wannan bayani shi ne, har yanzu zaman lafiya da bunkasuwa suna kasancewar babban take na wannan zamani, koda yake ana gamuwa da matsaloli wajen neman dunkulewar tattalin arzikin duniya, amma duk da haka ba za a canja wannan ra'ayi ba. A sa'i guda kuma, sabbin fasahohin zamani, da sabon halin sana'o'i da kuma sabon tsari da aka samar da su sakamakon yin kwaskwarima kan fasaha da masana'antu da ake yi na sabon zagaye, suna bukatar a tabbatar da su a kasuwannin duniya. Game da hakan, kasuwar kasar Sin na da makoma mai kyau, kuma kasar tana da niyyar kara habaka bude kofa ga ketare, wadannan sun kasance abubuwan da sauran kasashe ba su iya yi ba. Ban da wannan kuma, a fannonin hadin kan kasa da kasa dake jawo hankulan kasashen duniya a fannonin kawar da talauci, tinkarar sauyin yanayi, kiyaye zaman lafiya da dai sauransu, dukkansu na da alaka da ayyukan da Sin ta yi da gudummawar da ta bayar.
A saboda haka ne, a gun taron, an bukaci bangarori daban daban na kasar Sin da su "kara saurin kyautata tsarin tattalin arziki, da kafa karfin yin kirkire-kirkire kan kimiyya da fasaha, da zurfafa yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga ketare, da gaggauta neman ci gaba ta hanyar kiyaye muhalli, da kuma shiga ayyukan yin kwaskwarima kan tsarin gudanar da harkokin tattalin arzikin duniya". Ana iya tabbatar da cewa, wadannan fannoni biyar za su kasance muhimman ayyukan da kasar Sin za ta yi a lokacin samun damar neman ci gaba bisa manyan tsare-tsare, za kuma su kasance muhimmiyar hanyar da kasar za ta bi wajen mayar da matsin lamba zuwa karfin neman ci gaba.
Na uku, an tabbatar da wasu fannonin da za a dora muhimmanci a kai ta fuskar tattalin arziki a shekarar 2019.
Shekara mai zuwa shekara ce ta cika shekaru 70 da aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, ita ce kuma muhimmiyar shekara ta kafa zaman al'umma mai matsakaicin karfi da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta tabbatar. Don haka, yana da muhimmanci kwarai a yi kokarin raya tattalin arziki.
Taron ya yi nuni da cewa, babbar matsalar da kasar Sin take fuskanta ta fannin bunkasa tattalin arzikinta shi ne tsarin da ake bi na samar da kayayyaki, a game da wannan, ya kamata a kara daukar matakan da suka shafi kasuwanni da dokoki, ta yadda za a kawar da wasu masana'antun da suke samar da kayayyaki fiye da kima, da rage kudin da ake kashewa wajen gudanar da harkokin zaman al'umma, da kuma gaggauta samar da ingantaccen tsarin kasuwa na zamani. Taron ya kuma yi nuni da cewa, ya kamata a maida hankali a kan wasu fannoni bakwai, wato a inganta masana'antun kera kayayyaki da habaka kasuwannin cikin gida, da aiwatar da manufar farfado da karkara da bunkasa shiyyoyi daban daban cikin daidaito, da gaggauta gyare-gyaren tsarin tattalin arziki da inganta harkokin bude kofa daga dukkan fannoni, da kara inganta rayuwar al'umma.
Domin cimma burin da aka sanya gaba, taron ya kuma gabatar da wasu muhimman matakai. Misali, za a sake fasalin tsarin muhimman dakunan gwaje-gwaje na kasar, a kokarin inganta kwarewar masana'antun samar da kayayyakin kasar ta fannin kirkire-kirkiren fasahohi. An kuma gabatar da rage harajin da ma sauran kudaden da ake biya, a yunkurin inganta kwarewar masana'antu don raya kansu da kuma iyawar al'umma wajen sayen kayayyaki, ta yadda za a samar da wata babbar kasuwar cikin gida.
Yadda aka jaddada bukatar kafa wata kasuwar jari mai cikakken tsari, da gudanar da kome a fili ba tare da boye-boye ba, da bude kofa ga waje, na nufin kasancewar gyare-gyare a fannin kasuwar jari wani bangare ne mafi mihimmanci cikin tsarin gyarambawul da za a yiwa tsarin hada-hadar kudi ta kasar Sin a badi. Sa'an nan yadda aka nanata bukatar kare hakkin baki 'yan kasuwa dake kasar Sin, musamman ma hakkinsu wajen mallakar fasahohi, da yarda da kafuwar kamfanoni masu jarin waje a wasu fannoni, ya nuna imanin kasar Sin wajen kara bude kofarta, da kyautata muhalli na gudanar da harkokin kasuwanci.
Ko da yake, ci gaban tattalin arzikin kasar Sin na fuskantar yanayi mai sarkakiya, da yanayi na rashin tabbas, amma idan an waiwayi baya, za a ga tattalin arzikin kasar ya dade yana fama da wasu kalubaloli, kuma a karshe zai samu daidaituwar wannan yanayi tare da samun ci gaba, musamman ma a fannonin tinkarar kalubaloli, da kuma ingancin tattalin arziki. A watan Yulin bana, asusun lamunin duniya IMF ya sanar da wani rahoto kan tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2018, inda ya yarda da ci gaban da kasar Sin ta samu a kokarinta na gudanar da gyare-gyare a wasu manyan fannoni, haka kuma yana hasashen cewa tattalin arzikin kasar zai ci gaba da karuwa cikin sauri. A wajen taron tattalin arziki na kwamitin kolin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin na wannan karo, an sanar da wasu bayanai, da hasashen yanayin tattalin arzikin kasar a badi, inda aka nuna yiwuwar kasar wajen samun karin ci gaban tattalin arzikinta, gami da imanin da shugabannin kasar suka nuna kan yunkurinsu na raya kasa. Idan ana so a yi hasashe kan makomar tattalin arzikin kasar Sin, to, babu shakka za a iya ganin wata makoma mai haske. (Sanusi Chen, Jamila Zhou, Bilkisu Xin, Lubabatu Lei, Bello Wang)