190101-Waiwayen-wasu-muhimman-batutuwan-hadin-gwiwar-Sin-da-Afrika-a-shekarar-2018.m4a
|
A shekarar 2018, an gudanar da wasu muhimman tarukan hadin gwiwa na kasashen Sin da Afrika ta fuskar siyasa, ciniki da tattalin arziki, raya al'adu da dai sauransu, daga cikin muhimman tarukan da suka gudana, akwai taron kolin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika wanda aka fi sani da FOCAC wanda kasar Sin ta karbi bakuncinsa, wanda ya samu halartar kafatanin shugabannin kasashen Afrika da manyan jami'ai daga kasashen Afrika da sauran sassa daban daban na duniya. Taron FOCAC na Beijing 2018 yana daya daga cikin muhimman tarukan hadin gwiwa na Sin da Afrika wanda ya fi daukar hankalin duniya, musamman bisa la'akari da yadda mahukuntan bangarorin biyu suka mayar da hankali kan kyautata mu'amala da sada zumunta da kuma tabbatar da manufar nan ta samun moriya juna tare.
Bugu da kari, akwai taron bikin baje kolin Shanghai na kayayyakin da ake shigo da su daga kasashen duniya wato CIIE a takaice, wanda ya samu halartar kamfanoni sama da 3000 daga kasashen duniya da yankuna sama da 170 ciki, har da kasashen Najeriya, Ghana, Kenya da wasu kasashen Afrika da dama.
Ga yadda shirin ya kasance.