181227-wasannin-yara-a-makaranta-bello.m4a
|
A nan kasar Sin ana gudanar da wasu wasannin motsa jiki a makarantu ne da nufin kyautata lafiyar jikin yara. Yayin da ake gudanar da wasannin, a kan sa yara su yi guje-guje da tsalle-tsalle, da koyon wasu fasahohi na wasanni daban daban, ga misali, kwallon kafa, da kwallon kwando, da kwallon teburi na Pingpang, da wasan tsallake igiya, da dai sauransu. A wannan fanni, ina ga darassin PE da ake gudanar da shi a cikin makarantun kasar Sin ba zai sha bamban sosai da na kasar Najeriya ba.
Sai dai a nan kasar Sin, ban da sanya yara su shiga wadannan wasanni, akan kayyade wani matsayi da yara ya kamata su cimma gwargwadon shekarunsu na karfin jikinsu. Ga misali, dana yana da shekaru 6, yana wajen ajin farko na makarantar firamare. To, an kayyade cewa ya kamata shi da abokan karatunsa, su iya tsallake igiya har karo 100 a cikin minti guda. Bisa wannan manufa da hukumar ilimin kasar ta tsara, malaman makaranta suke sanya yara su dinga shiga horo, sa'an nan a karshe za su ci jarrabawar da za a yi musu, inda dukkansu za su yi kokarin tsallake igiya har fiye da karo 100 cikin minti daya.
Ban da wannan kuma, a cikin makarantun kasar Sin, a kan sanya dalibai su yi amfani da salon motsa gabobin jiki tare da kida wajen motsa jikinsu. Yayin da ake gudanar da wannan wasa, dalibai da yawa suna motsi iri daya tare da sautin wani kida. Wannan wasa yana ba su damar motsa gabobin jikinsu daya bayan daya. Haka kuma zai ba su damar koyon wasu al'adu na gudanar da wani aiki tare da wasu, inda za su yi kokarin bin sautin kida don samar da motsi iri daya. (Bello Wang)