in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar kasuwancin Sin: Tawagogin aikin Sin da Amurka suna tuntubar juna
2018-12-21 10:58:17 cri

Kakakin ma'aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar Sin Gao Feng ya gaskanta cewa, tawagogin aikin kasashe biyu wato Sin da Amurka, sun riga sun fara tuntubar juna, haka kuma suna tattaunawa kan batutuwan da za su yi shawarwari kan su. Gao Feng ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis a nan birnin Beijing

Kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng ya bayyana cewa, makasudin tuntubar juna tsakanin sassan biyu wato Sin da Amurka, shi ne kokarin warware sabanin dake tsakaninsu a fannin tattalin arziki da cinikayya, yana ganin cewa, muddin dai sassan biyu sun mai da hankali kan moriyar junansu, haka kuma sun yi kokari tare, za su iya tabbatar da matsaya guda da shugabannin kasashensu suka cimma yayin ganawarsu.

A farkon watan Disamban da ake ciki, shugabannin Sin da Amurka wato Xi Jinping da Donald Trump, sun gana a babban birnin kasar Argentina, inda suka amince da cewa, za su ingiza ci gaban huldar dake tsakanin kasashen su bisa tushen sulhuntawa, da hadin kai, da kuma kwanciyar hankali, kana sun cimma matsaya guda kan batun a fannin tattalin arziki da cinikayya, tare kuma da dakatar da karin harajin kwastam da kasashen biyu suke yi ga juna.

A yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi jiya, kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng ya bayyana cewa, tawagogin aikin Sin da Amurka suna tuntubar juna yadda ya kamata, yana mai cewa, "Tawagogin aikin sassan biyu za su yi shawarwari. Bayan da shugabannin kasashen biyu suka gana da juna a kasar Argentina, tawagogin aikin kasashen biyu su ma sun tattauna tsakaninsu sau da yawa, kuma nan gaba za su ci gaba da tattaunawa bisa bukatar aikin su, ta yadda za su tabbatar da matsaya guda da shugabannin kasashen biyu suka cimma."

Bisa labaran da aka buga a shafin intanet na ma'aikatar kasuwancin kasar Sin, an ce, a ranar 19 ga wata, tawagogin aikin sassan biyu, sun rika sun tattauna ta waya bisa matsayi na mataimakin minista, inda suka yi musanyar ra'ayi kan batutuwan da suka jawo hankulansu duka. Kakaki Gao Feng ya ce, yayin tattaunawarsu a wannan rana, manyan jami'ai biyu sun tattauna kan batutuwan dake shafar daidaiton cinikayya, da kiyaye ikon mallakar fasaha da sauransu, kana sun yi musanyar ra'ayi kan aikin da za su gudanar a kwanaki masu zuwa. Gao Geng ya bayyana cewa, muddin dai sassan biyu suka mai da hankali kan moriyar junansu, haka kuma suka yi kokari tare, za su iya tabbatar da matsaya guda da shugabannin kasashensu suka cimma yayin ganawarsu.

Abu mafi jawo hankalin jama'a shi ne, tun bayan da shugabannin kasashen Sin da Amurka suka cimma matsaya guda a farkon watan nan da ake ciki, hukumar kula da harajin kwastam ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta tsai da kuduri cewa, tun daga ranar 1 ga watan Janairu, har zuwa ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2019, kasar Sin za ta dakatar da kara harajin kwastam da take bugawa motoci, da kayayyakin motoci kirar Amurka, kudurin dake shafar kayayyaki guda 211. Kana ofishin wakilin cinikayya na kasar Amurka, shi ma ya jinkirta lokacin karin harajin kwastam da zai bugawa hajojin kasar Sin, wadanda darajarsu za ta kai dalar Amurka biliyan 200, daga kaso 10 bisa dari zuwa kaso 25 bisa dari, har zuwa tsakar daren ranar 2 ga watan Maris na shekarar 2019 dake tafe. Duk wadannan matakai da sassan biyu suka dauka sun nuna cewa, sassan biyu suna yin kokari tare domin warware sabanin dake tsakaninsu, Gao Feng ya bayyana cewa,"Yanzu sassan biyu sun riga sun dauki matakai, wadanda ke da muhimmanci matuka, game da warware sabanin dake tsakaninsu a fannin tattalin arziki da cinikayya."

Bana ce shekarar cika shekaru 40 da fitar da hadadden rahoton kulla huldar diplomasiyya dake tsakanin Sin da Amurka, kana adadin cinikayyar kayayyaki dake tsakaninsu ya kai dalar Amurka biliyan 580 a shekarar 2017, kana adadin cinikayyar aikin samar da hidima dake tsakaninsu shi ma ya kai dalar Amurka biliyan 120. Ban da haka gaba daya adadin jarin da sassan biyu suka zubawa juna a bara, ya kai dala biliyan 230.

A bayyane ne take cewa, huldar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu tana da muhimmanci matuka ga ci gaban huldar kasashen, Gao Feng ya ce, "Kasar Sin tana ganin cewa, moriyar sassan biyu a fannin tattalin arziki da cinikayya, ta fi sabanin dake tsakaninsu. Har kullum huldar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu tana da muhimmanci matuka ga ci gaban huldar kasashen biyu. A don haka dole ne a gudanar da huldar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu yadda ya kamata."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China