in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Algeria sun aika da sako ga juna don taya murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu
2018-12-20 14:30:33 cri
Yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na jamhuriyar jama'ar demokuradiyyar Algeria Abdelaziz Bouteflika, sun aika da sako ga juna don taya murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu.

A cikin sakonsa shugaba Xi ya nuna cewa, kasashen Sin da Algeria suna da dankon zumunci, kasar Sin kasa ce ta farko da ba ta kasashen Larabawa ba da ta amincewa da kasar Algeria, a nata bangaren ma kasar Algeria tana daya daga cikin kasashe na farko da suka kulla huldar diplomasiyya tare da sabuwar kasar Sin.

A cikin shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya, kullum kasashen biyu na samun cigaban dangantakarsu yadda ya kamata. A cewar Xi, yana fata bangarorin biyu za su ci gaba da hadin kai, kuma su mai da ranar ta cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya a matsayin masomi, na yada zumuncin gargajiya, da zurfafa hadin kai irin na samar da moriya ga juna, don inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi, hakan za a kara samar da gajiya ga jama'ar kasashen biyu.

A nasa bangaren ma, shugaba Bouteflika ya bayyana a cikin sakon cewa, ya gamsu kan ci gaban dangantakar dake tsakanin kasashen Algeria da Sin yadda ya kamaya a cikin shekaru 60 da suka gabata. A cewarsa, kullum kasashen biyu na nuna aminci ga juna, da nuna goyon baya ga juna, kuma sun samu cikakkiyar nasarar hadin kai a fannoni daban daban. Kasar Algeria na fatan ci gaba da inganta amincewar juna a fannin siyasa a tsakanin kasashen biyu, da sa himma wajen shiga ayyukan raya shawarar "Ziri daya da hanya daya", da kuma nuna goyon baya kan kafa al'umma mai kaykkyawar makoma ga duk bil Adama, ta yadda za a ciyar da dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni dake tsakanin kasashen biyu gaba.

A wannan rana kuma, firaministan kasar Sin Li Keqiang da takwaransa na kasar Algeria Ahmed Ouyahia su ma sun aika da sakon taya murna ga juna. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China