in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasa da kasa na maida hankali kan jawabin Xi a taron murnar cika shekaru 40 da yin gyare-gyare da bude kofa
2018-12-20 14:10:10 cri
Kasar Sin ta yi babban taron murnar cika shekaru arba'in da fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, kwanan baya a babban dakin taron jama'a dake birnin Beijing, inda shugaba Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi, wanda ya jawo hankalin kasashen duniya da dama.

Shafin intanet na jaridar Al-Ahram ta kasar Masar ya wallafa wani sharhi mai taken "Kasar Sin na murnar cika shekaru arba'in da aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje", inda ya yabawa manyan nasarorin da kasar Sin ta samu a cikin shekaru arba'in da suka gabata a fannonin samun ci gaba, da kwanciyar hankali da kuma samar da alheri ga jama'arta.

Sa'annan shafin intanet na Al-Masry Al-Youm na Masar ya bada sharhin cewa, yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen waje manyan manufofi ne da gwamnatin kasar Sin ke tsayawa wajen aiwatar da su a cikin shekaru arba'in da suka wuce, har ma akwai wasu kamfanonin kasar da dama wadanda suka samu dimbin nasarori a karkashin jagorancin gwamnatin kasar.

Ita kuwa jaridar Die Welt ta kasar Jamus ta ruwaito rahotanni ne dake cewa, a cikin shekaru arba'in, Sin ta samu babban ci gaba daga kasa mai dogaro kan ayyukan gona har ta zama kasa mafi karfin tattalin arziki ta biyu a duk duniya, har ma tana kara taka muhimmiyar rawa a harkokin duniya. Shugabannin kasar Sin sun fahimci cewa, fadada bude kofarta ga kasashen ketare, zai sanya sabon kuzari ga ci gaban tattalin arzikin kasar.

Har wa yau, wasu muhimman kafofin watsa labaran kasar Japan sun jinjinawa jawabin da shugaba Xi Jinping ya yi, inda suka ruwaito cewa, manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje ita ce ta taimaka sosai ga habakar tattalin arzikin kasar Sin gami da kyautatuwar zaman rayuwar jama'arta.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China