Wu Haitao, ya yi wannan kira ne yayin zaman kwamitin tsaron majalissar na jiya Laraba. Ya ce ci gaba da fuskantar wannan matsala ga kasashen, na barazana ga ci gaban su, da zamantakewar al'ummun su, tare da rura wutar tashe tashen hankula, da yaduwar ayyukan ta'adanci.
Ya ce batun fataucin miyagun kwayoyi, na bukatar hadin gwiwar kasashen duniya, da sauke nauyi daga ko wane bangare. Kaza lika akwai bukatar rufe kasuwannin kwayoyi, da hana shan su, da samar da su, da hada hadar su tun daga tushe.
Wu Haitao ya kara da cewa, ya zama wajibi a karfafa tsare tsaren aiwatar da manufofi tsakanin yankuna, da hukumomin kasa da kasa, da ma na MDD, ta yadda za a rika aiki tare. Ya ce Sin ta nuna yabo ga kokarin da suke yi wajen yaki da hada hadar miyagun kwayoyi, da tabbatar da aiwatar da dokoki masu nasaba da hakan, karkashin ka'idojin kasa da kasa. (Saminu)