in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hijira wata hanya ce mai karfi wajen bunkasa tattalin arziki, in ji babban jami'in MDD
2018-12-19 16:57:09 cri
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya fada a jiya Talata cewa batun yin kaura wata kakkarfar hanya ce wajen raya cigaban tattalin arziki.

"Yin kaura tana baiwa miliyoyin mutane sabbin damammaki wadanda zasu amfanawa al'ummar dake karbar bakuncin makauratan da kuma kasar 'yan kaurar ta asali," babban jami'in na MDD ya furta hakan ne a cikin sakon da ya aike na bikin tunawa da ranar makaurata ta kasa da kasa da aka gudanar a ranar 18 ga watan Disamba na kowace shekara.

Sai dai kuma, ya lura da cewa, "idan aka samar da dokoki marasa tasiri, batun yin kaura zai iya haifar da karuwar rarrabuwar kawuna a tsakanin al'umma, zai jefa mutane cikin cin zarafi da bautarwa, kana zai iya haifar da zubewar kimar gwamnatoci."

"A cikin wannan wata, duniya ta dauki wani babban mataki na cigaba, bayan da aka amince da yarjejeniyar batun yin kaura cikin lumana ta kasa da kasa" in ji shi, inda ya buga misali da yarjejeniyar doka ta farko da MDD ta amince da ita game da yadda za'a tinkari batun yin kaura a matakin kasa da kasa.

"Dokar wadda ta samu goyon bayan illahirin mambobin MDD, yarjejeniyar zata taimaka mana wajen magance ainihin kalubalolin dake shafar batun yin kaura tare da samar da babbar moriya," inji babban jami'in MDD.

Guterres ya nanata cewa "yarjejeniyar ta haskaka karin damammakin da suka shafi batun yin kaura bisa bin doka da oda, da kuma kwararan matakan dakile matsalolin da suka shafi yin safarar bil adama.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China