in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya bukaci a daga matsayin aikin kare hakkin dan adam
2018-12-19 12:03:44 cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres a jiya Talata ya yi kira da a daga matsayin aikin kare hakkin bil adama, yana mai cewa har yanzu akwai tafiya mai nisa duk da kasancewar an cika shekaru 70 tun bayan amincewa da yarjejeniyar MDD game da batun kare hakkin dan adam.

Mata, maza da kananan yara a duk fadin duniya har yanzu suna fuskantar matsin lamba, ko kuma tauye musu hakkokinsu. Muzgunawa, kisan kiyashi, tsarewa ba tare da hakki ba, da kuma sauran batutuwa da suka shafi cin zarafi da take hakkin dan adam. Mata da 'yan mata masu yawan gaske a kullum suna fuskantar rashin tsaro, cin zarafi da nuna wariya. A halin da ake ciki a yau muna ganin irin yadda ake fama da yawaitar mulkin kama karya, da muzantawa, da kashe kashe don nuna wariya da banbancin launi, inji mista Guterres.

Yarjejeniyar hakkin dan adam din ta zarce batu na samar da kwarin gwiwa kadai. Bangarori 30 dake kunshe cikin yarjejeniyar sun kunshi muhimman hanyoyin tabbatar da daga matsayin wanzar da zaman lafiya da kyautata matsayin kare hakkin dan adam, in ji shi. "Ta hanyar mutuntawa da daga matsayin kare hakkin dan adam ne kadai za'a cimma nasarar ajandar nan ta samar da dawwamamman cigaban dan adam nan da shekarar 2030."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China