in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da takardar manufofinta kan EU ta 3
2018-12-19 10:24:36 cri
Jiya Talata gwamnatin kasar Sin ta fitar da takarda ta 3, game da manufofin da take bi kan EU, takardar ta zo bayan takardu irin ta guda biyu da kasar ta fitar a shekarar 2003 da ta 2014.

Game da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying ta bayyana a yayin taron manema labaru da aka yi a wannan rana, cewa takardar muhimmiyar sanarwa ce da kasar Sin ta gabatar game da manufofinta kan EU, inda aka bayyana manufofi, da burin kasar kan EU a cikin sabon zamani, kuma muhimmin mataki ne da kasar ta dauka na karfafa shawarwari, da hadin kai a tsakanin Sin da EU a fannoni daban daban.

Baya ga haka, Hua ta bayyana cewa, EU muhimmin karfi ne a tsarin kasashen duniya, kana kasar Sin na mayar da hankali sosai kan amfaninta, da tasirin da take kawowa a harkokin shiyya-shiyya da na kasa da kasa, kuma raya dangantakar dake tsakaninta da EU ya kasance daya daga cikin muhimman ayyukanta wajen gudanar da harkokin diplomasiyya.

Ban da wannan kuma, Hua ta bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin na fatan zurfafa da habaka hadin kai a tsakaninta da EU a dukkan fannoni, da ciyar da dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu gaba, kana da yin kokari tare da EU don zama masu tabbatar da zaman lafiyar duniya, kuma masu ba da gudummowa kan ci gaban duniya, kana masu kiyaye tsarin kasa da kasa." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China