in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manufofin Diflomasiyar kasar Sin
2018-12-27 15:17:08 cri

Yayin da shekarar 2018 ke shirin karewa, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi cikakken bayani kan harkokin diflomasiyyar kasar Sin na shekarar bana, da kuma hasashe kan ayyukan diflomasiyyar kasar a shekara mai zuwa.

Wang ya bayyana cewa, a shekarar 2018, kasar Sin ta ci gaba da aiwatar da ayyukan diflomasiyyarta bisa hanyar da ta tsara, duk da matsalolin da ba za a rasa ba. Ya kuma yi bayani kan yadda kasar Sin take tafiyar da harkokin diflomasiyyarta cikin kalmomi guda shida, wadanda suka hada da, bude kofa ga waje, hadin gwiwa, samun ci gaba cikin kwanciyar hankali, jagoranci, sauke nauyinta da kuma tsayawa tsayin daka.

A farkon shekarar 2018, kasar Sin ta sanar da manufarta ta kara bude kofa ga waje yayin taron dandalin Boao na kasashen Asiya. A yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin za ta kara bude kofa ga waje, sa'an nan ya gabatar da jerin matakan da abin ya shafa domin cimma wannan buri.

A yayin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na farko da aka yi a birnin Shanghai a watan Nuwamba, jimilar kamfanoni 3600 daga kasashe, yankuna da kuma kungiyoyin kasa da kasa 172 ne suka halarci wannan biki. Kuma jimillar kudin ciniki da aka samar a yayin bikin ya kai yuan biliyan 60, lamarin da ya nuna aniyar kasar Sin wajen kafa tsarin ciniki mai bude kofa ga waje.

Batun kara bude kofa ga waje dai, shi ne babban aikin kasar Sin a fannin diflomasiyya a shekarar 2018. Yayin da ake fuskantar yaduwar ra'ayin kariyar ciniki, da na kashin kai da kuma cin zarafi a duniyarmu, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan shirin dunkulewar duniya waje guda, da tsarin ciniki cikin 'yanci, gami da manufar ba bangarori daban daban damar shiga a dama da su.

Manufar kasar Sin ta yin hadin gwiwa don tabbatar da moriyar juna, ita ce wadda ta fi janyo hankalin jama'ar duniya tsakanin manufofin hulda da kasashen waje da kasar Sin ta gabatar a shekarar 2018. Sauran fannonin diflomasiyar Sin a wannan shekara, sun hada da samar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin bil-Adama, da martaba dokoki da ka'idojin kasa da kasa da na MDD.

A sabuwar shekarar 2019, za a cika shekaru 70 da kafa sabuwar kasar Sin. Kasar Sin za ta gudanar da taron tattaunawa kan hadin gwiwar kasa da kasa da suka shiga shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" karo na biyu, da kokarin sada zumunta da yin hadin gwiwa a tsakanin ta da kasashen duniya, da tabbatar da zaman lafiya a yankin da ma a duniya baki daya, da kuma shiga aikin tafiyar da harkokin duniya da gudanar da manufofin diplomasiyya na musamman da ya dace da yanayin Sin a sabon zamani. Masana na cewa, wadannan manufofi sun tabbatar da kudurin kasar Sin na wanzar da zaman lafiya da samun wadata a duniya. (Ahmed, Samisu, Ibrahim /Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China