in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin Ta Fitar Da "Asirinta Na Samun Nasara", Ta Kuma Sa Niyyar Samun Karin Ci Gaba Nan Gaba
2018-12-18 19:52:29 cri

"Abin al'ajabi", "Sakamako ne da ba a taba samu ba a tarihin bil adama"……, sharhohi ne da gamayyar kasa da kasa ta kan yi kan manufofin yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga waje da kasar Sin take aiwatar. To, yaya aka kirkiro abubuwan al'ajabi? Mene ne suke kawo wa kasar Sin, har ma duk duniya baki daya? A yayin gagarumin taron murnar cika shekaru 40 da fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje da aka shirya a yau Talata, 18 ga watan Disamban, babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar Xi Jinping ya bayar da wani muhimmin jawabi, inda ya takaita ayyuka da sakamakon da kasar Sin ta yi a cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, da ma'anar aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga waje da kuma kyawawan fasahohin da kasar ta samu, sannan ya bayar da umurni ga dukkan 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da al'ummar Sinawa da su ci gaba da aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da kuma kara bude kofar kasar ga duk duniya gaba daya.

A cikin jawabinsa da ke kunshe da kalmomi fiye da dubu 10, shugaba Xi Jinping ya takaita sakamakon tarihi da kasar Si ta samu a cikin shekaru 40 da suka gabata a fannonin kafa tunani, da bunkasa tattalin arzikin kasa, da shimfida dimokuradiyya cikin harkokin siyasa da bunkasa al'adu, da kyautata zaman rayuwar al'umma da kare muhalli da zamanintar da rundunar tsaron kasa da yin kokarin dunkulewar dukkan yankin kasar baki daya da daidaita harkokin diflomasiyya cikin lumana da kuma raya jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Ya jaddada cewa, an samu sauye-sauye sosai na kasar Sin da na kabilu daban daban na kasar Sin da na Sinawa da kuma na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Jawabin da ya bayar ba tare da boye kome ba, kuma tare da imani na kunshe da dimbin abubuwa masu ma'ana, ba ma kawai sauran kasashen duniya za su iya fahimtar "asirin samun nasara" da kasar Sin take da shi sakamakon aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje ba, har ma za su iya sanin dalilin da ya sa shugabanni da jama'ar Sin suke da niyya da imani na kara yin gyare-gyare da bude kofar kasarsu ga ketare.

A lokacin da ake waiwayen ci gaban da kasar Sin ta samu cikin shekaru 40 da suka gabata sakamakon aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga ketare, za a iya fahimtar da dalilin da ya sa Sinawa suke jin alfahari a cikin zukatunsu. Yau da shekaru 40 da suka gabata, an kusa rushe tattalin arzikin kasar Sin, amma yanzu tattalin arzikin kasar ya zama mafi girma na biyu a duk fadin duniya. Sannan kasar Sin ta zama kasa mafi girma wajen samar da kayayyaki, da kuma fitar da kayayyaki zuwa kasuwannin duk duniya. Har ma gudummawar da kasar ke bayarwa ga ci gaban tattalin arzikin duk duniya ta kan kai fiye da kashi 30 cikin dari a cikn jerin shekaru da dama da suka gabata. Bugu da kari, a da, Sinawa su kan fuskanci matsalar rashin abinci da tufafi, amma yanzu yawan mutanen da suka fito daga kangin talauci ya kai miliyan 740. Matsakaicin kudin da kowane Basine ke kashewa a duk shekara ya kai kudin Sin Yuan dubu 26, kwatankwacin dalar Amurka dubu 4. Yawan mutane masu matsakaiciyar rayuwa yana ta karuwa.

Daga wata kasa wadda babu wanda yake nuna amincewa gare ta, zuwa wata kasa wadda gamayyar kasa da kasa suke dauke ta mai ba da babbar gudummawan kan kiyaye zaman lafiyar duniya da kuma inganta bunkasuwar duniya, kasar Sin ta kashe shekaru 40 wajen canja ra'ayoyin kasashen duniya kan ita. Har masanin kasar AMurka Samuel Huntington ya nuna cewa, lalle manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje ta ba da babbar gudummawa ga bunkasuwar kasa ta Sin.

Cikin jawabinsa, shugaba Xi ya ce, babbar nasarar da kasar Sin ta cimma a fannin masana'antu cikin shekaru 40 da suka gabata, ta yi daidai da nasarar da kasashe masu ci gaba suka cimma cikin shekaru darurruka da suka gabata. Mu al'ummomin kasar Sin mun kammala wani babban aiki mai nauyi da ba wanda ya taba yi cikin tarihi ba.

Kuma me ya sa Sinawa suka iya cimma wannan nasara? Shugaba Xi ya ce, sabo da kokari da gwarin gwiwa da kuma basirarmu ne! sa'an nan, shugaba Xi Ya takaita muhimman fasahohin da kasar Sin da samu a fannoni guda 9 cikin shekaru 40 da suka gabata, ya kuma jaddada cewa, ya kamata mu ci gaba da bin wadannan ka'idoji a nan gaba domin neman ci gaban kasar.

Wadannan fasahohi suka hada da, ya kamata mu bi jagorancin Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, mu mai da ayyukan dake shafar jama'ar kasa a matsayin ayyuka mafi muhimmanci namu, mu ci gaba da bin tsarin gurguzu na kasar Sin, kyautata wannan tsari, yayin da dukufa wajen neman bunkasuwa, kara bude kofa ga waje da kuma gudanar da harkokin JKS yadda ya kamata da dai sauransu.

Ko shakka babu, wadannan fasahohin da kasar Sin ta samu su zama mafi janyo hankulan gamayyar kasa da kasa. Sabo da yadda kasar Sin take aiwatar da harkokin yin kwaskwarima da neman bunkasuwa ya iya zama abin koyi ga kasashe masu tasowa. Bisa kididdigar da aka yi, tun daga shekaru 1980, ya zuwa yanzu, kimanin kasahen Asiya da Turai guda 30 sun canja tsarin tsararren tattalin arziki nasu zuwa tsarin tattalin arziki iri na kasuwanci, amma ya zuwa shekarar 1997, ma'aunin tattalin arziki na GDP na gabalin daga cikinsu, ba su kai matsayi na shekarar 1989 ba. kuma babban dalilin da ya sa haka shi ne, ba su iya daidaita alakar dake tsakanin yin kwaskwarima da neman ci gaba.

Cikin jawabinsa, shugaba Xi ya yi bayani kan fasahohin kasar Sin, yana mai cewa, ya kamata mu nuna himma da kwazo wajen yin kwaskwarima, yayin da tabbatar da ci gaban kasar cikin yanayin zaman karko. Sa'an nan, mu hada ayyukan yin kwaskwarima da neman ci gaba cikin yanayin zaman karko yadda ya kamata, domin mu dukufa wajen bin shirimmu ne neman ci gaban kasa.

Ya jaddada cewa, " Mene ne za mu gyara, kuma ta yaya za a yi gyare-gyaren? Ya kamata mu tabbatar da batun bisa tsarin gurguzu mai halayyar musamman na kasar Sin, da burinmu na daidaita tsarin kula da kasa, da zamanintar da dabarunmu a fannin kula da kasa. Za mu gyara wanda za mu iya gyara, sa'an nan mu magance taba wurin da bai kamata a canza ba. " Wannan magana ta sanya manufar gyare-gyare da bude kofa ta kasar Sin ta zama kan wata daidaitaciyar turba.

Bayan wadannan shekaru 40, ana wajen wani sabon mafari ga tarihin kasar Sin: A wani bangare, taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19 ya samar da wani babban buri na kara raya tattalin arziki da zaman al'umma a kasar, inda aka tsara matakan da za a bi na kafa al'umma mai walwala, da zamanintar da fannoni daban daban, da kokfa wata kasa mai karfi da ke bin tsarin gurguzu. A dayan bangaren kuma, ra'ayoyi na kare kai, da kashin kai sun fara bullowa da kansu a duniya, lamarin da ke hana ruwa gudu ga yunkurin dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda, da kara haifar da wani yanayi na rashin tabbas ga muhallin dake wajen kasar Sin. Dangane da lamarin, Xi Jinping ya ce kasar Sin tana cikin wani yanayi na kara fuskantar wuya yayin da take neman ci gaba, kuma ba za ta iya koma baya ba, saboda haka, imani ya zama wani abu dake da matukar muhimmanci. Shugaban ya yi furucin ne don tunasar da jama'ar kasar Sin, gami da karfafawa 'ya'yan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da daukacin al'ummar kasar gwiwarsu, domin su ci gaba da aiwatar da manufar gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje.

Yayin da ake kokarin aiwatar da manufar, za a iya fuskantar wasu ayyuka masu wuyar gaske, wadanda suke baiwa masu nazarin al'amuran duniya na kasashen waje mamaki. Duk da haka, kasar Sin ta fahimta cewa, yayin da ake aiwatar da gyare-gyare da neman ci gaba a wata babbar kasa mai tarihi na shekaru fiye da dubu 5, da yawan al'ummarta na fiye da biliyan 1.3, ba zai yiwu ba a samu wata cikakkiyar dabarar da za a koya, ko kuma wanda zai nuna ma jama'ar kasar Sin yadda za a yi. Kawai za a dogaro kan imani da kokarin aiki. Idan an yarda cewa, nasarorin da kasar Sin ta samu cikin shekaru 40 da suka wuce sun ba mutanen duniya mamaki, to, a shekaru 40 ko fiye masu zuwa, kasar Sin za ta tabbatar da gaskiyar hasashen da shahararren masanin ilimin tattalin arziki wanda ya samu kyautar Nobel Ronald H. Coase ya ci, wanda ya ce: " Kasar Sin da ta bude kofarta, da nuna hakuri, da imani da kai, gami da kokarin kirkiro sabbin fasahohi, za ta baiwa mutanen duniya karin mamaki." (Masu Fassarawa: Sanusi Chen, Maryam Yang, Bello Wang, ma'aikatan sashen Hausa na CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China