in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#Gyare-gyare da bude kofa#Ya zama dole kasar Sin ta nace ga tsarin gurguzu da ke da sigar musamman ta kasar Sin
2018-12-18 12:19:23 cri
Babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping a yau Talata ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, tsarin gurguzu da ke da sigar musamman ta kasar Sin, tsari ne da dole ne kasar Sin ta tsaya tsayin daka a kai. Ya ce, babban ma'aunin da za a bi wajen gudanar da gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje shi ne, duba kan ko gyare-gyaren za su taimaka ga inganta tsarin gurguzu da ke da sigar musamman ta kasar Sin, kuma ko za su taimaka ga tsarin gudanar da harkokin kasa. Ya ce kasar Sin za ta tsaya ga gudanar da gyare-gyaren da suka dace, amma ko kadan ba za su yi gyare-gyaren da ba su kamata ba. Ya kuma jaddada cewa, ya kamata kasar Sin ta sanya matukar muhimmanci a kan aikin bunkasa tattalin arziki, ta kuma nacewa ga manyan ka'idoji biyar, tare kuma da tsayawa tsayin daka, ga yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje.
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China