in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Somali da dakarun tsaron AU zasu hada kai don murkushe al-Shabab
2018-12-17 10:39:06 cri
Tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika a Somalia (AMISOM) da jami'an tsaron kasar Somali sun yi wani shiri na hadin gwiwa don kaddamar da aikin soji a yankin tsakiyar Jubba, dake kudancin kasar domin kakkabe maboyar mayakan al-Shabab.

Charles Tai Gituai, mataimakin kwamandan tagawar dakarun tsaron AU mai kula da aikin sintiri da tsara dabaru, ya bayyana a cikin wata sanarwa a jiya Lahadi cewa, aikin na hadin gwiwa zai kunshi dakarun tsaron AMISOM, da na jahar Jubbaland da kuma dakarun sojin kasar Somali (SNA).

Gituai wanda ya kuma jagoranci wata tattaunawa da manyan kwamandojin tawagar jami'an tsaron ta AU dake Kismayo, ya yabawa dakarun bisa jajurcewar da suka nuna da kuma sadaukar dakai wajen gudanar da aikinsu wanda hakan ya bada babbar gudunmowa wajen tabbatar da zaman lafiya a jahar Jubbaland.

Shiyyar Middle Jubba an yi amannan shine yanki daya tilo da ya rage wanda mayakan al-Shabab ke amfani dashi a matsayin mafakarsu.

A cewar tagawar dakarun tsaron AU, mayakan sun rasa sukuni inda suke ta kokarin kaddamar da harin sari ka noke domin kare kansu. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China