in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin Ta karfafawa Sinawa gwiwar Su rika Motsa Jiki
2018-12-20 14:36:17 cri

Sin ta gabatar da wata manufar karfafawa Sinawa gwiwar motsa jiki, don inganta lafiyarsu, musamman matasa da yara. Sin ta bukaci kowane Sinawa da ya rika shiga ayyukan motsa jiki a kalla sau daya a kowace rana, da koyon hanyoyin motsa jiki biyu, da kuma ba su shawarar yin binciken lafiyar jikinsu a kowace shekara. Don me kasar Sin ta gabatar da wannan manufa?

An zartas da dokar wasanni ta farko ta kasar Sin a shekarar 1995, a wannan shekara majalisar gudanarwar kasar Sin ta gabatar da shirin karfafawa Sinawa gwiwar motsa jiki, daga baya an gabatar da jerin dokoki da ka'idojin wasanni. Binciken da hukumar wasanni ta kasar Sin ta gudanar ya nuna cewa, yawan Sinawa da su ke motsa jiki ya kai kashi 33.9 cikin dari na adadin Sinawa da shekarunsu ya kama daga 7 zuwa 70, kuma kashi 60.7 cikin dari na mazaunan biranen kasar suna motsa jiki a cikin kungiyoyin wasanni iri iri.

Karkashin wannan shiri na karfafawa Sinawa gwiwar motsa jiki na shekaru 15, bullo da tsarin samar da hidimar motsa jiki ga jama'a shi ne burin gwamnatin kasar. Ya zuwa yanzu, akwai dakukuwan wasanni kimanin dubu 616 a kasar Sin, jama'a suna iya amfani da yawacinsu. Kana an kafa wuraren motsa jiki a kusa da rukunin gidaje ko unguwanni, da wuraren yawon shakatawa, da filayen ciyayi, da gefen tituna da sauransu, inda aka samar da na'urorin motsa jiki a wadannan wuraren. Alal misali, an bullo da ayyukan motsa jiki da suka dace da ma'aunin kasar a dukkan unguyoyin jama'a da garuruwa.

Ya zuwa karshen shekarar 2003, yawan kudin da hukumar wasanni ta kasar Sin ta zuba ga shirin karfafawa Sinawa gwiwar motsa jiki ya kai kudin Sin Yuan biliyan 1. Tun daga shekarar 2001, hukumar wasanni ta kasar Sin ta yi amfani da tikitin cacar mai rabo ka samu wajen gina cibiyoyin motsa jiki na gwajin a dukkan biranen Sin 31 ciki har da Dalian, da Beijing, da Changchun da sauransu. Kana an zuba jarin kudin tikitin cacar mai rabo ka samu na kasar Sin a yankin yammacin kasar Sin da yankin babbar madatsar ruwan kogin Yangtsi da ke koma bayan ci gaban tattalin arziki don taimaka musu wajen gina ayyukan motsa jiki na jama'a, wadanda za su amfanawa garuruwa da birane 101.

Ayyukan karfafawa Sinawa gwiwar su rika motsa jiki a kasar Sin, sun taimaka wajen canja tunanin rayuwar Sinawa sosai. A wasu manya da matsakaitan birane na kasar, aikin kiwon lafiya da motsa jiki dake samun karbuwa sun taimaka wajen inganta rayuwar jama'a sosai a kasar Sin. Wasu sabbin wasanni kamar wasan hawa duwatsun bango, wasan gudu a kasa da katako mai taya, wasan alkafura daga sama, wasan tae kowndo, wasan kwallon lambu, wasan kwallon daran teburi, wasan kwallon bowling, wasan hawan dawaki, wasan damben mata da sauransu sun fi jawo hankalin matasa sosai. A karshen shekarar 2003, an fara gina filin wasan kwallon lambu a kan kankara na farko na kasar Sin a birnin Arxan dake yankin Mongoliya ta gida na kasar Sin, wannan shi ne filin wasan kwallon lambu a kan kankara na shida a duniya, wanda aka zuba jari Yuan biliyan 1 wajen gina shi.

Karkashin wannan shiri na karfafawa Sinawa gwiwar motsa jiki daga shekarar 2016 zuwa 2020 da aka tsara, jama'ar kasar Sin sun fi son yin motsa jiki, da yawansu ya karu sosai. Kuma yawan mutanen da suke motsa jiki fiye da sau daya a kowane mako zai kai miliyan 700, kana yawan mutanen da su kan motsa jiki zai kai miliyan 435, hakan zai kara inganta lafiyar jama'ar kasar. Manufar karfafawa Sinawa gwiwar su motsa jiki ta taimaka matuka ga bunkasuwar sha'anin wasannin motsa jiki, da zama sabon fannin bunkasa tattalin arziki.

Bisa yadda aka tsara wannan shiri, daga shekarar 2016 zuwa 2020, za a gudanar da ayyuka a fannoni biyar. Na farko, za a inganta wasannin motsa jiki na yau da kullum kamar gudu, da tafiya da kafa, da hawa keke, da hawa duwatsu, da wasan iyo, da wasan kwallo iri iri, da yin raye-raye a fili da sauransu, da kokarin inganta sabbin wasannin motsa jiki na zamani kamar wasan jiragen ruwa mai filafilai, wasan takobi, tseren motoci, wasan hawa dawaki, da sauransu, da kuma nuna goyon baya ga yada wasannin gargajiya na kasar Sin kamar wasan Wushu, da wasan Tai Chi, da wasan Qigong da kuma wasu wasannin motsa jiki da ake yi a kauyukan kasar Sin. Kuma ana kokarin gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta jama'a a wurare daban daban na kasar Sin bisa yanayin wuraren.

Na biyu, kokarin gina ayyukan motsa jiki na jama'a, da bullo da tsarin ayyukan motsa jiki a birane da yankuna da garuruwa da kauyuka, da yawan filayen motsa jiki na kowane mutum da zai kai muraba'in mita 1.8, da kyautata ayyukan motsa jiki iri iri ciki har da ayyukan motsa jiki na nakasassu. Hakazalika kuma, za a tabbatar da bude filayen wasanni na kamfani ko hukumomin gwamnati ko na makarantu ga dukkan al'ummar kasar.

Na uku, kokarin yin amfani da sabbin fasahohin zamani wajen inganta sha'anin wasannin motsa jiki, kamar tattara sakwanni game da yanayin motsa jiki, da horar da mutane dabarun motsa jiki ta hanyar kallo hotunan bidiyo a kan internet da sauransu.

Na hudu, a maida hankali ga samar da hidimar wasannin motsa jiki ga kowa da kowa cikin adalci. Za kuma a taimakawa yankunan kananan kabilu, da wadanda ke kan iyaka, da na masu fama da talauci da su raya sha'anin karfafa Sinawa gwiwar yin motsa jiki. Kana a maida hankali ga matasa da yara da rika halartar wasannin motsa jiki don inganta lafiyar jikinsu. Ya kamata a kara koyar da darussan wasannin motsa jiki a makarantu, kana makarantu su mayar da hankali wajen inganta aikin lafiyar jikin matasa da yara da bullo da tsarin kiwon lafiya da tsara lokutan motsa jiki a makarantu, kana da amfani da matsayin lafiyar dalibai a matsayin muhimmin ma'aunin ciyar da malaman makarantu gaba.

Kana ya kamata a yi kokarin samar da wuraren motsa jiki ga tsofaffi a unguwoyi, da taimakawa ayyukan wasannin motsa jiki da suka dace da yanayin tsofaffi, da samar da horo da hidima ga tsofaffi a fannin motsa jiki yadda ya kamata.

Hakazalika kuma, za a kara nuna goyon baya ga sha'anin wasannin motsa jiki na nakasassu, da karfafawa mutane masu nakasassu gwiwar shiga wasannin motsa jiki da inganta lafiyar jikinsu yadda ya kamata.

A gaggauta raya wasan kwallon kafa da wasannin kankara, da kara gina filayen wasan kwallon kafa da wasannin kankara, don karfafawa jama'a gwiwar su kara shiga wadannan wasanni, da cimma burin maida mutane miliyan 300 shiga harkokin wasannin kankara da Sin ta tsara.

A halin yanzu, motsa jiki ya kasance wani muhimmin bangare na rayuwar jama'a, don haka ya kamata a kara gudanar da ayyukan karfafawa Sinawa gwiwar shiga wasannin motsa jiki a kasar don inganta lafiyar jama'a, kana motsa jiki zai zama muhimmin dandalin yin mu'amala da juna da more fasahohi da juna a zamantakewar al'ummar kasar.

Don biyan bukatun jama'a na ganin suna motsa jiki a kasar Sin, majalisar gudanarwar kasar ta zartas da kuduri a shekarar 2008 cewa, tun daga shekarar 2009, ranar 8 ga watan Agustan kowa ce ta kasance ranar motsa jiki ta kasar Sin. An shirya gudanar da bukukuwa da dama a wanann rana don karfafawa Sinawa gwiwar su kara motsa jiki da yada dabarun wasannin motsa jiki ga kowa da kowa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China