A makon da ya wuce ne a birnin Alkahira, babban birnin kasar Masar, aka soma gudanar da shirin ba da tallafin hadin kai na kasar Sin, mai taken"Kowa ce mace da kowane yaro"da MDD ta gabatar, an gudanar da shirin ne da nufin cimma burin kyautata lafiyar mata da yara, wanda ya kasance daya daga cikin muradun ci gaba kafin shekarar 2015 na MDD, kana da ba da tallafi ga masu fama da larura na kasashen Afirka dake fama da talauci da wadanda ke karancin kayan jinya, ciki har da kasar Masar.