in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya suna kallo matakin kasar Canada za ta dauka
2018-12-13 13:37:32 cri

A ranar 11 ga wata ne, babbar kotun lardin British Columbia na kasar Canada ya ba da belin sako Madam Cathy Meng, babbar darektar kula da harkokin kudi ta kamfanin Huawei na kasar Sin. An dai ba da belin Madam Cathy Meng kan dallar Canada miliyan 10, da kuma kadarar gida da tsabar kudi. Ban da haka kuma, babbar kotun ta bukaci mutane biyar da za su tsayawa Madam Cathy Meng.

Ba da belin sakon Madam Cathy Meng ya dan kwantar da hankalinta, da ma iyalinta, kamfaninta, al'ummomin kasar Sin da ma gamayyar kasa da kasa, wadanda suka damu matuka kan halin da take ciki. Kuma wannan mataki da kasar Canada ta dauka ya dace kwarai da gaske.

Amma, 'yancin Madam Cathy Meng ta samu wani muhimmin mataki ne mai nauyi kuma na dogon lokaci dake gabanmu. Rahotannin kafofin watsa labaran kasar Canada na cewa, kasar Amurka za ta iya gabatar da iznin tusa keyar Madam Cathy Meng zuwa kasarta kafin ranar 8 ga watan Janairu na shekarar 2019. A sa'i daya kuma, za a sake sauraren shari'ar Madam Cathy Meng a kasar Canada a ranar 6 ga watan Fabrairu na shekarar 2019. Idan kasar Canada ta tusa keyar Madam Cathy Meng kasar Amurka, mai iyuwa ne Amurka za ta yanke mata hukuncin zaman wakafi na shekaru 30.

Kamfanin Huawei ya shiga kasuwannin kasar Canada ne a shekarar 2008, kafofin watsa labaran kasar Canada na nuna cewa, kamfanin Huawei bai taba aikata wani laifi a kasar ba, kana, kamfanin ya kafa wasu hukumomin nazari a biranen Ottawa, Toronto, Waterloo da wasu wuraren kasar, wadanda suka samar da guraben aikin yi sama da dari 5 ga wannan kasa. Haka kuma, kamfanin Huawei ya taba zuba jari a wani shirin talebijin mai farin jini na kasar Canada.

A ranar 1 ga watan Disamba ne kasar Canada ta kama Madam Cathy Meng kamar yadda Amurka ta bukata, abun da ta yi rashin hankali ne, kuma tabbas ne za ta dandana kudarta kan wannan laifin da ta aikata, idan har ba ta gaggauta sakin Madam Cathy Meng ba.

Haka kuma, wannan laifin da kasar Canada ta aikata ya bata dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, lamarin da zai gurgunta burinta na kara fitar da kayayyakinta zuwa kasar Sin, da kuma kara shigar masu yawon shakatawa na kasar Sin zuwa kasarta. Don haka, ya kamata kasar Canada ta sake tunani kan matakan da za ta dauka, domin kar ta haddasawa kanta matsala.

Wasu kasashen yammacin duniya ba sa goyon bayan kamfanin Huawei, bisa zargin cewa, kamfanin yana da dangantaka mai kyau da gwamnatin kasar Sin, kuma wani sojan da ya yi ritaya ne ya kafa wannan kamfani. Lamarin da ya sa, kamfanin Huawei ya kasance kamfanin Sin dake fuskantar bincike a kasashen ketare. Amma, ba a taba samun labarin cewa, kamfanin ya taba aikata harkokin da ba su dace ba. Kasar Canada ta san da wannan sosai.

A hakika, zargin da aka yi wa kamfanin Huawei ba domin ya boye wani abu ba ne, sai don bunkasuwarsa cikin sauri ta damu wasu kasashen duniya.

Baya ga haka, wasu kafofin yada labarai na kasa da kasa sun yi nuni da cewa, dalilin da ya sa Amurka ta bukaci Canada ta kama Madam Cathy Meng shi ne don neman dakile kamfanin Huawei, ta yadda za ta kawo cikas ga ci gaban kasar Sin ta fannin kimiyya da fasaha, kuma wannan matakin babu kunya a cikinsa.

Tabbas kasar Canada ta san da haka, amma gwamnatin kasar ta zabi bin umurnin kasar Amurka, ta tsare 'yar kasar Sin Cathy Meng, lamarin da ya keta 'yanci da kuma dangantakar dake tsakanin Sin da Canada. Sabo da haka, ya kamata kasar Sin ta mayar mata martani, domin kare daidaituwar dangantaka a tsakaninta da kasar Canada, ta kuma kiyaye tsarin kasa da kasa mai adalci.

Kamar yadda aka sani, kasar Amurka ta kan kakaba takunkumi ga manyan shugabannin kamfanonin kasashen ketare, a wannan karo, kasar Canada ta taimaka mata, ta tsare shugabar kamfanin Huawei wadda ba ta taba aikata wani laifi ba, lamarin da zai bata sunan kasar Canada, da sanya damuwa ga manyan shugabannin kamfanonin ketare dake kasar Canada.

A saboda haka, ya kamata kasar Canada ta gaggauta gyara kuskuren da ta aikata, saboda yadda ta bata dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin baki daya, da kuma kiyaye yanayin adalci na duniya, da tabbatar da 'yancin cinikin tsakanin kasa da kasa, ta yadda za ta samu girmamawa daga kasa da kasa, a maimakon taimakawa wata kasar da take son aiwatar da kariyar ciniki a duniya.

Muna fatan kasar Canada za ta warware wannan batu da idon basira, ta saki Madam Cathy Meng cikin sauri, sabo da a halin yanzu, dukkanin al'ummomin kasa da kasa sun zuba ido su ga yadda lamarin zai kaya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China