181212-Taron-sauyin-yanayi-na-Poland.m4a
|
A ranar Litinin uku ga watan Disamban shekarar 2018 ne, aka bude taron sauyin yanayi na MDD a birnin Katowice dake kasar Poland, taro mafi muhimmanci tun bayan da aka daddale yarjejeniyar birnin Paris, kuma yin shawarwari game da yadda za a aiwatar da yarjejeniyar zai yi tasiri ga yadda ake aiwatar da yarjejeniyar ta Paris, da ma batun tinkarar matsalar sauyin yanayi a duniya baki daya.
Babban sakataren MDD António Guterres ya yi nuni cewa, bisa rahoton bambancin fitar da abubuwa masu gurbata yanayi na shekarar 2018, wanda hukumar kiyaye muhalli ta MDD ta gabatar a watan Nuwamba a halin yanzu alkawuran da kasashen duniya suka yi na rage fitar da abubuwa masu gurbata yanayi bai kai burin da aka tsara nan da shekarar 2030 bisa yarjejeniyar Paris ba. Don haka,akwai bukatar kasashen duniya su sake duba alkawuran da suka yi a yarjejeniyar ta Paris don cimma wannan burin nan da shekarar 2030.
Tawagar wakilan kasar Sin a taron ta yi wa taron manema labaru bayani game da ka'idoji da matsayin kasar Sin a gun taron cewa, Sin tana kula da shawarwari kan ka'idojin aiwatar da yarjejeniyar Paris a fannoni uku, wato tabbatar da gama yin shawarwarin cikin lokaci, da fahimta, da aiwatar da yarjejeniyar Paris yadda ya kamata, da kuma aiwatar da yarjejeniyar a dukkan fannoni cikin adalci, da kuma maida hankali ga muhimman fannoni。
Masu fashin baki na ganin cewa, batun tinkarar sauyin yanayin duniya, ba batu ne na siyasa ba kawai, wannan al'amari ne na tattalin arziki. Don haka, muddin ana bukatar yarjejeniyar ta taka rawar da ta dace a kokarin da ake yi na magance matsalar sauyin yanayin duniyar da muke ciki, wajibi ne kasashe da kungiyoyin da abin ya shafa su cika alkawarin da suka dauka daga dukkan fannoni. (Saminu, Ahmed, Ibrahim/Sanusi Chen)