Huang Kunming, wanda shi ne memba a ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban sashin fadakar da jama'a na kwamitin tsakiya na jam'iyyar, ya yi wannan furuci ne yayin da yake ganawa da wasu kwararru da masana daga kasashen waje a gun taron karawa juna sani dangane da darrusan tattalin arziki dake tattare da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje da kasar Sin ta fara aiwatarwa shekaru 40 da suka gabata, wanda aka yi jiya Lahadi, a jami'ar Tsinghua dake birnin Beijing.
Huang ya bayyana cewa, manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje ba taimakawa ci gaban kasar Sin kadai ta yi ba, har ma da samar da alfanu ga duk duniya baki daya. Ya ce Sin za ta ci gaba da tsayawa kan aiwatar da wannan muhimmiyar manufa.(Murtala Zhang)