Da yake karin haske cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, Mr. Le ya bayyana cewa, abin da Amurkar ta yi, ya saba wa 'yanci da muradun al'ummar kasar Sin kana ba ya bisa turba.
Jami'in ya ce, kasar Sin ta yi Allah wadai da matakin na Amurka,don haka tana kira ga bangaren Amurka da ya dora muhimmanci kan matsayin kasar Sin ya kuma gaggauta daukar matakan da suka dace don gyara kura-kuran da ya tafka, ya kuma janye sammacin kama 'yar kasar Sin da ya bayar.
Le ya ce, kasar Sin za ta mayar da martani kan matakin da bangaren Amurkar zai dauka.(Ibrahim)