in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hakkin wa Canada take karewa?
2018-12-09 17:15:06 cri

Jami'an tsaron kasar Canada sun kama madam Meng Wanzhou, wadda ita ce babbar jami'ar dake kula da harkokin kudi wato CFO a takaice, ta shahararren kamfanin Huawei mai zaman kansa na kasar Sin a filin saukar jiragen saman kasar, bisa bukatar kasar Amurka a ranar 1 ga wata, daga baya kuma, wato a ranar 7 ga wata, agogon wurin, an shirya taron jin ra'ayin jama'a domin gurfanar da madam Meng a kotun birnin Vancouver na kasar ta Canada, amma kuma bayan taron da ya shafe tsawon awoyi biyar, ba a yanke hukunci kan batun ba, inda aka jinkirta zuwa gobe Litinin.

Batun kama madam Meng Wanzhou a Canada, ya jawo hankalin al'ummomin kasashen duniya, haka kuma ya sa kamfanin Huawei da al'ummun kasar Sin da kuma gwamnatin kasar mamaki matuka, har al'ummumomin kasashen duniya baki daya sun yi ta kai suka kansa. Daga batun, an lura cewa, kasar Canada ta dauki matakin da bai dace ba, kuma ko shakka babu za ta yi fama da matsalar da batun zai haifar:

Da farko, za a iya gano cewa, kasashen Amurka da Canada suna nuna fin karfi da rashin kunya a gaban al'ummomin kasashen duniya, duk da cewa sun taba bayyana cewa, ana aiwatar da manufofin adalci da cikakken tsarin dokoki a kasashensu.

Rahotanni na cewa, jami'an tsaron Canada sun kama Meng Wanzhou ne bisa dalilin sabawa umurnin sakawa kasar Iran takunkumi na kasar Amurka, amma nan take kamfanin Huawei ya fitar da wata sanarwa, inda ya bayyana cewa, kamfanin ya bi daukacin dokokin kasashen da yake gudanar da harkokinsa, haka kuma Amurka ta sabawa dokar kasa da kasa bisa sakawa Iran takunkumi. A ranar 3 ga watan Oktoban bana, kotun kasa da kasa na MDD ta yanke hukuncin cewa, sakawa Iran takunkumi da Amurka ta yi, ya sabawa yarjejeniyar sada zumunci a fannonin huldar tattalin arziki da hakkin diplomasiyya da kasashen biyu suka daddale a shekarar 1955, har ta bukaci Amurka ta dakatar da matakin nata nan take. A karkashin irin wannan yanayi ne kuma, Amurka ta sanar da cewa, za ta soke wannan yarjejeniya. A bayyane yake cewa, Amurka tana daukar matakin da bai dace ba kan kamfanin da bai sabawa doka ba.

Game da Canada kuwa, tabbas ta san yanayin da ake ciki, amma ta bayyana cewa, batun ba shi da nasaba da harkar siyasa ko kadan, a sanadin haka an mayar da gwamnatin Canada matsayin yar amshin shata, wato mai bin umarnin kasar Amurka.

Na biyu, Canada tana gurgunta hakkin dan Adam kamar yadda take so, ko shakka babu za ta kawo illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasashen duniya.

Kamar yadda aka sani, Canada mamba ce ta kungiyar leken asiri ta kasashe biyar wato Amurka da Birtaniya da Australia da Canada da New Zealand wato Five Eyes a takaice, mambobi biyar suna musayar bayanai a tsakaninsu, hakan ya sa al'ummomin sauran kasashe suke jin tsoro, har suke ganin cewa, batun kama Meng Wanzhou da Canada ta yi, ya nuna cewa, tana barazana ga hakkin dan Adam har tana take su kamar yadda take so.

Na uku, ana ganin cewa, Canada ta dauki matakin ne domin lalata moriyar kamfanin fasaha mafi girma na kasar Sin.

A baya, Canada ta taba nuna adawa da takunkumin da Amurka ta sakawa Iran, amma yanzu tana bin umurnin Amurka, inda kuma a fakaice take amfani da wannan dama wajen gurgunta moriyar kamfanin Huawei. Daga nan an gano cewa, hakika Canada ita ma tana son lalata kamfanin, wanda ya nuna rinjayi matuka wajen samar da na'urorin sadarwa a fadin duniya.

A halin da ake ciki yanzu, kamfanonin kasar Sin suna taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban tattalin arzikin duniya, a don haka wasu kasashe ke yin amfani da matakan siyasa domin hana bunkasuwar kamfanonin, wasu kuwa suna ikirarin cewa, ana gudanar da gogayya bisa tushen adalci, amma a sa'i daya suna lalata muhallin gogayyar adalci, domin tabbatar da moriyarsu, amma sau tari an samu shaidu daga tarihi cewa, makarkashiyarsu za ta bi ruwa.

Yanzu kamfanin Huawei da gwamnatin kasar Sin sun bukaci gwamnatin Canada da ta saki madam Meng Wanzhou nan take ba tare da bata lokaci ba, ana sa ran cewa, gwamnatin Canada da hukumomin shari'ar kasar za su daina aikin da suke yi wanda ya sabawa doka da adalci.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China