in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sarhi: Me ya sa ake bukatar hangen nesa kafin a samu tabbatar da makomar tattalin arzikin duniya?
2018-12-01 21:35:24 cri

Xi Jinping, shugaban kasar Sin, ya yi wani muhimmin jawabi a wajen taron mataki na farko na taron kolin kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki G20, a jiya Jumma'a, inda ya yi kira ga shugabannin kasashe mambobin kungiyar da su "yi hangen nesa, don sauke nauyin dake bisa wuyansu, da tabbatar da makomar tattalin arzikin duniya". Ban da haka, ya bukace su da su nuna karfin zuci, da tsayawa kan manufar "bude kofa da hadin kai, da taimakawa juna, don samar da wasu sabbin dabarun da za su amfanawa kowa", ta yadda za a samu a raya tattalin arzikin duniya bisa madaidaiciyar hanya.

Cikin shekaru 10 da suka wuce, taron koli na kungiyar G20 ya taka muhimmiyar rawa wajen daidaita yanayin tattalin arzikin duniya. Zuwa yanzu, yayin da shugabannin mambobin kungiyar suka sake taruwa don tattauna batun tattalin arzikin duniya, suna fuskantar wani mawuyacin hali, wato tattalin arzikin duniya ka iya kara tabarbarewa, sa'an nan zartar da ra'ayi na radin kai, da kare kai, suna barazana ga tsarin da ake bi yanzu na kula da ra'ayi da moriyar kowane bangare. Yanzu kasashe daban daban za su yi wani zabi, wato ko su ci gaba da bin tsarin dunkulewar duniya waje guda, da kokarin habaka ciniki cikin 'yanci, da karfafa hadin gwiwa maimakon sabani da juna, Ko kuma su nuna son kai wajen kare moriyar kai maimakon ta duk duniya, da yayata ra'ayi radin kai, da kariyar ciniki, sa'an nan a haddasa tashin hankali a duniya?

Ma iya cewa za su yi wani zabi mai muhimmanci matuka, domin kansu gami da tattalin arzikin duniya. Wannan zabin da za a yi na bukatar shugabannin kasashe daban daban da su nuna hangen nesa, da sanin ya kamata, maimakon lura da yanayin da ake ciki yanzu kawai.

Don ci gaba da gudanar da manufar bude kofa da hadin gwiwa, ya kamata kasashe daban daban su yi kokarin kare ciniki cikin 'yanci, gami da tsarin cinikayya da ya shafi bangarori daban daban, wanda aka kafa shi bisa tushen ka'idojin kasa da kasa, musamman ma ka'idodjin da aka gabatar karkashin laimar kungiyar ciniki ta duniya WTO. Cikin wadannan ka'idoji, an bayyana komai a fili, tare da tabbatar da matakan hukuncin da za a iya dauka, don samar da sauki ga cinikin da ake yi tsakanin kasashe daban daban. A sa'i daya, kungiyar WTO ta samar da wani tsari da za a iya bi don daidaita sabanin ra'ayi a fannin ciniki, ta yadda za a samu damar magance tashin hankali da wutar yaki.

Abin bakin ciki shi ne, a shekarun baya, kungiyar WTO na ta fuskantar barazanar zartar ra'ayin radin kai da kare kai. Ga misali, akwai kasar da ta yanke hukunci ga abokanta na ciniki bisa dokokin kanta maimakon ka'idojin kasa da kasa, har ma ta karbi karin harajin kwastam kan kayayyakin sauran kasashe. Wannan mataki ya haifar da matsin lamba ga gudanar kungiyar WTO, gami da yin zagon kasa ga tsarin ciniki da ya shafi bangarori daban daban. Game da wannan batu, Mauricio Macri, shugaban kasar Argentina, wanda ke karbar bakuncin taron G20 na wannan karo, ya ce ana ta kokarin kai hari ga tsarin cinikin da ake bi, wanda ya shafi bangarori daban daban, cikin 'yan shekarun da suka gabata.

A yayin taron, shugabannin kasashen BRICS da suka hada da Sin, Rasha, Indiya, Brazil da kuma Afirka ta Kudu sun gana, inda suka cimma ra'ayi daya cewa, ya kamata a nuna goyon baya ga kungiyar WTO da kuma tsarin cinikin dake tsakanin kasa da kasa, domin tabbatar da ciniki tsakanin kasa da kasa mai bude kofa ga waje da adalci da kuma gudanar da komai a bayyane.

Idan muka yi waiwaye, za mu iya gane cewa, a shekarar 2008 wato lokacin da aka yi fama da matsalar cinikin duniya, an farfado da tattalin arzikin duniya bisa hadin gwiwar mambobin kungiyar G20 da daidaita manufofin tattalin arziki da kuma kawar da kariyar ciniki. Wani muhimmin sakamakon da aka samu shi ne "Yin hadin gwiwa domin warware matsala", don haka yanzu bai kamata a manta da wannan sakamako ba.

Ko shakka babu, hadin gwiwar mambobin kungiyar G20, wadanda gaba daya GDP nasu ya kai 85% cikin karfin tattalin arzikin duniya, za ta yi babban tasiri kan bunkasuwar tattalin arzikin duniya, da kuma zaman takewar al'umma baki daya.

Sabo da haka, wakilan kungiyar EU sun bayyana a yayin taron kolin G20 cewa, sakamakon da aka samu a shekarar 2008 ya nuna cewa, ta hanyar yin hadin gwiwa, za a iya warware dukkan kalubalen da za a gamu da su, da kuma tabbatar da ci gaban tattalin arzikin duniya cikin zaman karko, ta yadda za a kiyaye tsaro da bunkasuwar kasa da kasa. Shi ya sa, dukkan kasashen BRICS da mambobin kungiyar EU suka nuna aniyarsu ta ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a nan gaba.

Cikin taron koli na wannan karo, shugaban kasar Sin XI Jinping ya kuma yi kira ga shugabannin kungiyar 20 da su sabunta fasahohin da abin ya shafa domin neman sabuwar dama ta raya tattalin arziki. Kuma mene ne muhimmiyar ma'anar sabuntawa a yayin da ake neman karuwar tattalin arziki?

Masanin tattalin arziki wanda ya taba lashe lambar yabo ta Nobel Edmund Phelps ya taba yin nazari kan tushen dalilan da suka tabbatar da ci gaban tattalin arziki da kuma bunkasuwar zaman takewar al'umma cikin littafinsa mai taken "Mass Flourishing", inda ya bayyana cewa, duk da manufofin tattalin arziki, kudi da na ciniki suna tasiri kan bunkasuwar tattalin arziki da zaman takewar al'umma, sa kaimi ga jama'a da su sabunta fasahohinsu ya ba da karin gudummawa ga karuwar tattalin arizki. Abun nufi shi ne, sabunta fasahohi ita ce jigon inganta karuwar tattalin arziki.

Neman samun ci gaba yana da muhimmanci matuka, amma 'yan siyasa wadanda suke da tunanin neman samun ci gaba bisa ka'idar taimakawa juna ba su da yawa, har ma wasu 'yan siyasa na kasashen yammacin duniya sun dauki matakan nuna adawa da neman bunkasar tattalin arzikin duniya baki daya. Wani babban dalilin da ya sa suka yi haka shi ne, karuwar gibin dake kasancewa tsakanin masu arziki da marasa arziki. Yin ciniki cikin 'yanci da neman bunkasar tattalin arzikin duk duniya baki daya sun sanya kungiyoyin tattalin arziki na duniya samun moriya, inda wasu daga ciki suka samu da yawa, wasu kuma suka samu kadan, yayin da wasu suka gaza samun ko kadan, ya sa wasu yin shakku da kuma nuna adawa da bunkasar tattalin arzikin duk duniya baki daya. Idan 'yan siyasa ba sa son sauke nauyin dake bisa wuyansu kamar yadda ya kamata, akwai yuwuwar yin ciniki maras shinge da kuma bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya su zama masu laifi da jama'a za su nuna bakin cikinsu gare su sakamakon mawuyacin halin tattalin arziki da suke ciki.

A cikin jawabin da ya gabatar a yayin taron G20, Xi Jinping ya nuna cewa, "yanzu ana fuskantar matsaloli iri daban daban a duk duniya, amma dukkansu suna da nasaba da batun neman ci gaba." Dole ne "a bi ka'idar cimma nasara da moriyar kowa da kowa tare". Shugaba Xi ya ce, bayan barkewar rikicin hada-hadar kudi na kasa da kasa shekaru 10 da suka gabata, gudummawar da kasar Sin ta bayar ga karuwar tattalin arzikin duk duniya ta kai fiye da 30%. Ko da yake yanzu tattalin arzikinta ya samu ci gaba cikin sauri, amma gwamnatin kasar Sin ta sanya aikin kawar da talauci da ya zama daya daga cikin ayyuka mafi muhimmanci da za ta kammala, har ma ta tsai da kudurin kawar da talauci a shekarar 2020 bisa ma'aunin da ake bi yanzu. Amma wannan wani abin misali ne dake bayyana yadda gwamnatin kasar Sin take hakuri da batutuwa iri daban daban a lokacin da take mai da hankali kan batun neman ci gaban kasar.

A cikin wadannan shekaru 10 da suka gabata, a kullum kasar Sin na kokarin zurfafa aikin yin gyare-gyare a gida da kuma kara bude kofarta ga ketare. Alal misali, ta kafa yankunan yin cinikayya marasa shinge guda 12 daya bayan daya a duk fadin kasar. Wasu matakan yin gyare-gyare da ta dauka a 'yan watannin da suka gabata, suna kuma jawo hankulan duk duniya sosai. Alal misali, ta dakatar da matakan kayyade shigar jarin waje a kasuwannin hada-hadar kudi da inshora da samar da motoci da kera jiragen sama da dai makamatansu. Sakamakon haka, kamfanin inshora na Allianz da na BASF sun samu izinin kafa rassasu masu zaman kansu, kuma ba sa bukatar neman jarin bangaren kasar Sin a cikin rassan dake nan kasar Sin.

A lokacin da ake bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya, "sannu a hankali kasashen duniya za su kasance kamar kawayen dake da moriya iri daya, ko suke sauke nauyin dake bisa wuyansu tare, har ma suke da makoma iri daya. Ko da yake za a gamu da matsaloli iri iri kan hanyar neman ci gaba, kara yin hadin gwiwa irin ta moriyar juna ita ce zabi daya tilo da za a iya yi." Duk wanda yake son sanya kansa gaba da wasu, ko daukar matakin da bangare daya ne ke samun riba, ta yadda daya bangaren tilas ya yi hassara, mai yiyuwa ya samu moriya cikin gajeren lokaci, amma za su kawo illa sosai ga bunkasar tattalin arzikin duk duniya cikin dogon lokaci mai zuwa, har ma su kawo cikas ga kokarin neman ci gaba nan gaba.

Kowace kasa za ta sha magani sakamakon hasarar tattalin arziki. Idan ana son kama daidaitacciyar hanyar neman ci gaban tattalin arzikin duk duniya, kowa na bukatar yin hangen nesa, musamman 'yan siyasa na kasashen duniya. (Masu Fassawara: Sanusi Chen, Bello Wang, Mariyam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China