Jami'an diplomasiyya na ziyarar kauyen Yantong na gundumar Dali (mai daukar hoto: Shui Lianhua)
A shekarun baya, gundumar Dali ta garin Weinan dake lardin Sha'anxi na kasar Sin, ta riga ta zama wata shahararriyar cibiyar samar da kayan lambu da 'ya'yan itatuwa, ta hanyar raya aikin gona, musamman ma fannonin samar da dabino da sauran 'ya'yan itatuwa, da raya aikin kiwon kifi da sauran dabbobi. Yayin da tattalin arzikin wurin ke samun ci gaba cikin sauri, zaman rayuwar mazauna wurin shi ma ya kyautata.
A ranar 30 ga watan Oktoban bana, bisa wani shiri na gayyaci jami'an diplomasiyya na kasashe daban daban dake kasar Sin, domin su ziyarci birnin Weinan na lardin Sha'anxi, wasu jami'an diplomasiyya na kasashen Afirka ta Kudu, Iran, Tanzania, Rwanda, Somaliya, Mauritius, sun kai ziyara a kauyen Yantong, da kauyen Pingluo, da kauyen Changjia dake gundumar Dali, inda suka nuna niyyar taimakawa kulla huldar hadin gwiwa tsakanin manoman wurin da 'yan kasuwar kasashensu, ta yadda za a baiwa gundumar Dali damar fitar da amfanin gona zuwa kasashen waje.
An ce kauyukan gundumar Dali na da kyan muhalli, kana manoman wurin na cike da imani
A wata na 9 bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, an riga an wuce lokacin shan aiki a cikin gonaki, don haka an ga mazauna kauyen Yantong da yawa da suke hira a wajen wani filin dake tsakiyar kauyen, sa'an nan kauyen na cikin wani yanayi na natsuwa. Sai dai zuwan jami'an diplomasiyyar ya janyo hankalin jama'ar wurin, tare da samar da wani yanayi na kwaramniya. Wasu daga cikin mazauna wurin sun daga hannayensu don jinjinawa baki, wasunsu sun ce "Hello", kalmar da ta ta da dariya tsakanin jama'ar wurin, domin hakika ba su san yaren Turanci ba. Duk da haka kishi da kauna da jama'a suka nuna sun burge jami'an diplomasiyyar sosai, har ma sun yi musafaha da jama'ar, gami da daukar hoto tare da su.
Banyan da jami'an suka shiga cikin gidajen manoman wurin, sun duba wurin kwana da dakin girki, har ma sun gwada zama kan gadon da ke iya dumama kansa. Jami'an diplomasiyyar sun nuna sha'awa sosai kan zaman rayuwar mazauna kauyen, har ma sun dinga tambaya cewa, "Mene ne wannan?" "Mene ne amfanin wannan abu?" "Kudin nawa ne ake kashewa domin gina gida irin wannan?" "Akwai mutane nawa a cikin iyalinku?"… Sa'an nan mutanen da suka taimakawa jami'an diplomasiyyar wajen tafinta, su ne tsohon jakadan kasar Sin a kasar Gabon Sun Jiwen, gami da uwargidansa Yang Baozhen, inda suka yi cikakken bayani kan fannoni daban daban na zaman rayuwar manoman, wadanda suka hada da kayayyakin da ake amfani da su wajen dafa abinci, da dabarar da ake bi wajen raya tattalin arzikin kauyuka.
Karamar jakadar musamman mai cikakken iko ta kasar Afirka ta Kudu dake kasar Sin Balatseng Debora Mmaseneo tana hira da manema labaru (Mai daukar hoto: Zhang Jingpan)
Karamar jakadar musamman mai cikakken iko ta kasar Afirka ta Kudu dake kasar Sin Balatseng Debora Mmaseneo, ta bayyana a yayin da take zantawa da 'yar jaridar CRI-Online cewa, a ganinta, al'ummomin wurin suna jin zaman rayuwarsu a garin kwarai, suna kuma da gidaje masu kyau, da kuma na'urorin zaman rayuwa masu inganci a cikin gidajensu. A nasa bangaren kuma, jami'in diflomasiyyar ofishin jakadancin kasar Tanzaniya dake kasar Sin Laizer Joseph Stephen ya bayyana cewa, yana son mutanen garin sosai, sabo da suna da mutunci. A ganinsa, suna zaman rayuwa cikin jin dadi da zaman lafiya.
Masu ziyara sun nuna aniyarsu ta karfafa hadin gwiwa
A garin Pingluo wanda yake kusa da garin Yantong, ana raya ayyukan gona na zamani cikin yanayi mai kyau. An gina gadinar rani da fadinsu ya kai muraba'in mita dubu dari 4, da babbar rumfa da aka gina da karfe mai muraba'in mita miliyan 1, har ma da babbar rumfar furanni guda uku a wannan gari, domin kara kudin shigar manoman wurin ta hanyar raya ayyukan gona da yawon shakatawa.
A shekarar 2017, kudin shiga na kowane mutam a garin ya kai Yuan 13650, a halin yanzu, garin ya kasance abin koyi a fannin bunkasuwar ayyukan gona na zamani, da kuma yanayin zaman rayuwa na gari.
Bayan ziyararsa a babbar rumfar furanni, da kuma shan 'ya'yan itatuwa na garin, Mashawarcin jakadan kasar Somaliya dake kasar Sin Ali Mohamed Hussein ya tambayi mai garin Chaoyi cewa, "Ko za mu iya yin hadin gwiwa?"
"Ko shakka babu!" mai garin ya amsa masa.
'Yar jaridar CRI-Online tana yin intabiyu da Ali Mohamed Hussein, mashawarcin jakadan kasar Somaliya dake kasar Sin (Mai daukar hoto: Shui Lianhua)
Sa'an nan kuma, mashawarcin jakadan ya kara da cewa, kasar Somaliya kasa ce ta noma, gabilin mutane suna zaune a kauyuka, inda suke samar da 'ya'yan itatuwa iri-iri, amma ba su iya samun kudin shiga da yawa ba, sabo da karancin fasahohin gona na zamani. Yana mai cewa, "Ina fatan za mu iya koyon fasahohi na garin nan, domin taimakawa kasar Somaliya wajen raya tattalin arzikinta".
Jami'in diflomasiyyar ofishin jakadancin kasar Tanzaniya dake kasar Sin Laizer Joseph Stephen yana daukar hotuna da mazauna garin Yantong (Mai daukar hoto: Shui Lianhua)
Shugabar hukumar hadin gwiwar tattalin arziki da fasahohi ta gundumar Dali Zhang Huanling ta bayyana cewa, muna sa ran karfafa hadin gwiwa tsakaninmu da kasashen Afirka, kuma za mu gabatar da tsarin karfafa hadin gwiwa tsakaninmu cikin sauri, domin aiwatar da manufofi na dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC da aka yi a birnin Beijing yadda ya kamata.