in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yanayi da makomar kwallon kafar Jamus
2018-11-29 15:35:17 cri

Bisa dukkanin alkaluma, ana iya cewa shekarar bana bata yiwa kasar Jamus kyau a fannin kwallon kafa ba. Ba za a manta da rashin nasara da kasar ta ci karo da ita, a yayin gasar cin kofin duniya na farkon shekarar nan ba, inda aka fitar da kungiyar kasar tun a farkon gasar, kana ta fada zuwa matsayi na biyu, wato rukunin B a ajin kwararru na kwallon kafar kasar.

To ko wadanne irin kura-kurai kungiyar ta aikata, kuma ta yaya zakarun na gasar cin kofin duniya a shekarar 2014, karkashin jagorancin kocin su Joachim Loew za su shawo kan wannan matsaloli?

Matakan dauka

Ya zama dole ga kocin kungiyar mai shekaru 58 da haihuwa, ya matsa kaimi wajen farfado da kungiyar sa. Ko da wasan karshe da kungiyar ta buga a gasar cin kofin duniya da ya gabata, ya nuna a fili irin rauni da kungiyar ke da shi. Ga alama koci Loew ya yi kasa a gwiwa, wajen nazartar yanayin sauyi da kwallon kafa ke ciki a duniya. Ya jima yana makale da tsaffin 'yan wasan kasar, tare da maida hankali ga buga salon wasan da aka dade da sanin kasar da shi.

Ga alama dai akwai bukatar gudanar da babban sauyi a tsarin taka ledar kasar, wanda zai dace da yanayin da ake ciki a yanzu. Kuma dole ne a yarda da cewa, lokacin haskawar taurarin kasar irin su Thomas Muller, da Jerome Boateng 'yan wasan Bayern Munich, da Sami Khedira na Juventus ya wuce. Kaza lika dole ne Mats Hummels na Bayern ya fuskanci takara daga matasan 'yan wasa da ake da su a yanzu. Ana ma dai iya cewa, Toni Kroos na Real Madrid ne kadai Jamus din ba za ta iya sauyawa a halin yanzu ba.

Duk da irin rashin nasara da kasar Jamus ta kwasa a baya bayan nan, wasu na ganin koci Loew bai amince da bukatar yiwa kungiyar kasar cikakken garan bawul ba. Maimakon hakan, kocin ya maida hankali ga dawowa da salon kungiyar na shekarar 2018, lokacin da ta buga gasar cin kofin duniya tare da kasar Faransa wadda ita ce ta lashe gasar, inda yake amfani da 'yan baya masu kwarewa, da 'yan gaba masu saurin kai farmakin ramuwar gayya, tare da taimakon masu taimakawa wajen kwato kwallo cikin sauri.

DAMAMMAKIN LOEW

Wasan da kungiyar kasar ta Jamus ta tashi kunnen doki 2 da 2 tare da Holand a baya bayan nan, na nuna irin yadda Jamus din ke dogaro da 'yan wasanta matasa su 3. Wato Leroy Sane na Manchester City, da Serge Gnabry na Bayern Munich, da kuma Timo Werner na RB Leipzig, kungiyar da fari ita ke rike da wasan, inda ta kai ga cin kwalle 2 ba ko daya, ta kuma yi asarar wasu karin damammakin ma na jefa karin kwallaye.

Masu goyon bayan kungiyar sun nuna mamaki, ganin yadda Werner ne kadai aka je da shi gasar cin kofin duniya cikin wadannan 'yan wasa.

Kuma bayan maye gurbin Gnabry da Werner, sai Jamus ta rasa tagomashin ta na sauri, da mamaye wasan, hakan ya haifar da farke kwallayen da aka zura mata maimakon nasarar da ta fara samu.

Wasu alkaluma sun nuna cewa, wadannan 'yan wasa matasa su uku, na da sauri da kwarewar mamaye wasa, wanda hakan ka iya taimakawa kungiyar a dukkanin wasan da za ta buga.

MAKOMAR LOEW

Duk da makoma mai haske da ake ganin kungiyar ta Jamus na da ita, Ana ci gaba da sanya ido kan kocin kasar ta Jamus. Da fari dai, hukumar kwallon kafar kasar ta bukaci ganin kungiyar ta ci gaba da kasancewa a rukuni A, wato na ajin kwararru dake kasar. Hakan kuwa na da nasaba ne da rashin wani zabin na daban, kuma hakan ya sanya Loew ci gaba da rike mukamin sa har zuwa wannan gaba, amma rashin samun gurbin buga gasar cin kofin kasashen turai na shekarar 2020 mai zuwa, abu ne da mahukuntan kwallon kafar kasar ba za su amince da shi ba.

WASU DABARUN KYAUTATA KWAREWAR KUNGIYAR

Ko shakka ba bu kungiyar kwallon kafar Jamus, ta rasa mogoya bayan ta da dama. Ko da rashin karsashi da aka gani a bangaren magoya bayan kungiyar a filin wasa na Leipzig, yayin da kungiyar ta tashi wasa 3 da nema ita da takwarar ta ta Rasha a farkon watan nan, alama ce dake nuna rashin jin dadin magoya bayan tamaula a kasar.

Haka ma wasan kungiyar da Holand a filin wasa na AufSchalke dake Gelsenkirchen. Yayin da magoya bayan Holland ke ta rera wakoki na nuna goyon baya, su kuwa magoya bayan Jamus tsit kake ji, ba wani karsashi ko nishadi tare da su. A shekarun da suka gabata, wasa tsakanin kasashen biyu kan dauki hankali matuka, amma a shekarar bana, masu goyon bayan Jamus sun shiga wani hali na rashin kuzari.

Yayin da Loew ke fuskantar yanayi na bukatar kara azama domin gobe, ita ma hukumar dake kula da harkar wasan kwallon Jamus na da rawar takawa, wajen kara inganta hazakar 'yan wasan kasar, ba tare da bata lokaci ba. Sashen hukumar na bukatar kocin kungiyar, da 'yan wasan sa, su sauya akalar kungiyar zuwa wani yanayi da kowa zai yi farin ciki da shi a shekarar dake tafe ta 2019. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China