in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha sun taimaka wajen samar da ci gaba mai dorewa a Sin
2018-11-28 10:51:28 cri

Jiya Talata mataimakin ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin Xu Nanping ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, nacewa ga manufar samun dauwamammen ci gaba ita ce matsaya guda daya da aka cimma a duk fadin duniya, ita ma kasar Sin tana nacewa ga manufar yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha domin inganta rayuwar al'ummar kasar tare kuma da kyautata yanayin kasar baki daya.

An kaddamar da muradun samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030 na MDD a shekarar 2016 a hukumance, inda aka yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakai domin cimma burin samun ci gaba mai dorewa a fannonin zamantakewar al'umma da tattalin arziki da kuma muhalli a fadin duniya.

A matsayinta na kasar da ta sa hannu kan muradun, kasar Sin ta fitar da rahoto game da ci gaban da ta samu kan aikin aiwatar da muradun samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030 na MDD a shekarar 2017 kafin sauran kasashen duniya, inda ta bayyana matakan da ta dauka da kuma sakamakon da ta samu a fannin.

Mataimakin ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin Xu Nanping ya bayyana yayin da yake zantawa da manema labarai jiya a nan birnin Beijing cewa, a fannin kimiyya da fasaha, kasar Sin ta riga ta samu ci gaba mai gamsarwa, musamman wajen samun ci gaba mai dorewa, yana mai cewa, "A baya mun yi amfani da hanyoyi daban daban domin samun ci gaban kasa, amma tun daga shekarar 2015, a kai a kai muna kara mai da hankali kan aikin yin kirkire-kirkire domin cimma burin samun ci gaba mai dorewa a kasar da ma fadin duniya baki daya, mun lura cewa, MDD ta sha kiran taruruka da dama wadanda suka samu mahalarta daga kasashen da za su amfana daga kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, ana iya cewa, kasashen duniya sun cimma matsaya kan manufar samun ci gaba mai dorewa ta hanyar yin kirkire-kirkire."

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, har kullum kasar Sin tana mai da hankali matuka kan aikin yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha, haka kuma an yi nuni yayin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 da cewa, yin kirkire-kirkire zai ciyar da tattalin arzikin kasar gaba yadda ya kamata.

Xu Nanping yana ganin cewa, kokarin da kasar Sin take yi kan aikin yin kirkire-kirkire ya dace da bukatun ci gaban tattalin arzikin kasar, haka kuma ya dace da bukatun ci gaban duniya, yana mai cewa, "Me ya sa akan ce aikin kimiyya da fasaha yana da muhimmanci matuka ga ci gaban kasar Sin a halin da ake ciki yanzu? Hakika lamarin yana shafar ci gaban tattalin arzikin kasar, a don haka kasar Sin tana goyon bayan aikin yin kirkire-kirkire sosai."

Xu Nanping ya kara da cewa, tun bayan da aka fara aiwatar da manufar yin gyaran fuska a gida da bude kofa ga ketare shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin ta samu babban ci gaba kan aikin kimiyya da fasaha, duk da cewa an gamu da matsaloli da dama, nan gaba, kasar Sin za ta kara kokari domin kara bude kofarta ga kasashen waje a wannan fannin, tare kuma da taimakawa masu aikin kimiyya da fasaha, yana mai cewa, "Bai kamata a takaita aikin masana kimiyya da fasaha da 'yan kasuwa da manufofin da aka tsara ba, saboda hakan zai hana su yin kirkire-kirkire, abu mai faranta ran mutane shi ne majalisar gudanrwar kasar Sin tana kokari wajen kafa kamfanoni da yin kirkire-kirkire a cikin shekarun baya bayan nan, ina ganin cewa, ya dace kowa da kowa ya saba da kirkire-kirkire a rayuwarsu ta yau da kullum."

Xu Nanping ya jaddada cewa, daga fasahohin da aka samu, an lura cewa, ko da yake saurin ci gaban tattalin arziki yana da muhimmanci, amma abu mafi muhimmanci shi ne samun ci gaba bisa tushen zaman jituwa tsakanin tattalin arziki da zamantakewar al'umma, yanzu haka kasar Sin tana kara mai da hankali kan samun ci gaba mai dorewa, yana mai cewa, "Dole ne a daidaita matsalar rashin daidaito dake tsakanin saurin ci gaban tattalin arziki da aikin kiyaye muhalli, a cikin shekarun baya bayan nan, ya kamata mu rage yawan kayayyakin da muke samarwa, domin kiyaye muhalli, kan wannan, ina ganin cewa, ya dace mu tattauna da hukumomin MDD da abin ya shafa domin kara kyautata tunanin raya kasarmu, misali saurin ci gaba, da alakar dake tsakanin ci gaban tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al'umma da sauransu."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China