181128-Ranar-yaki-da-cutar-AIDS-ta-duniya.m4a
|
Ana bikin wannan rana ce a ranar 1 ga watan Disamban kowace shekara domin ilimantar da jama'a game da cutar, illolinta, abubuwan dake haddasa yaduwarta, matakan kariya da sauransu.
Bugu da kari, wannan rana, wata dama ce ga jama'a a duniya baki daya su hada kai a kokarin da ake yi na yaki da cutar, nuna wa masu dauke da cutar goyon baya, tare da tunawa da wadanda suka kwanta da ma sanadiyar cutar.
Wannan rana, ita ce rana ta farko a duniya da ta shafi harkokin kiwon lafiya kuma an fara bikin ranar ce a shekarar 1988.
Bayanai na nuna cewa, ya zuwa shekarar 2017, cutar ta hallaka mutanen da yawansu ya kama daga miliyan 28.9 zuwa miliyan 41.5. Baya ga mutane miliyan 36.4 dake dauke da kwayar cutar. Wannan ya nuna cewa yawan wadanda cutar ke hallakawa ya ragu a shekarar 2005 daga miliyan 1.9 zuwa miliyan daya.
Tarihi ya nuna cewa, daga lokacin da aka bullo da shirin yaki da cutar Sida na majalisar dinkin duniya (UNAIDS) a shekarar 2004, shirin ya himmatu wajen ilimantar da jama'a tare da zabar take ko jigon da zai kasance a ranar yaki da cutar ta kowace shekara ta hanyar tattaunawa da sauran kungiyoyin lafiya na duniya.
Masu fashin baki na cewa, muddin ana bukatar yaki da cutar ta kanjamau, wajibi ne a samar da magungunan rage karfin cutar ga masu fama da ita, magance tsangwama da wariyar da ake nuna musu, sannan jama'a su tsaya ga iyalansu da daukar matakan da masana kiwon lafiya suka zayyana don kariya daga kamuwa da wannan cuta mai hallaka jama'a. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)