An dai zabo mutanen ne daga sassan rayuwa daban daban, sun kuma samu shaida daga matakai na tushen al'umma, kana an gudanar da tantancewa domin tabbatar da sahihancin zaben na su.
Wadanda za a karrama din sun kunshi masana a fannin kimiyya, da masana tattalin arziki, da 'yan JKS da suka yi fice a matakai na tushe, da wadanda suka yi fice a fannin kwadago. Sauran sun kunshi manajojin kamfanoni, da mamallaka sana'o'i masu zaman kan su.
A bana ne dai kasar Sin ke cika shekaru 40, tun bayan fara aiwatar da manufofin gyare gyare a cikin kasar, da kuma bude kofar ta ga sauran kasashen duniya.