181121-Nune-nunen-ci-gaban-kasar-Sin-cikin-shekaru-40-da-suka-gabata.m4a
|
Shekarar 2018, shekaru arba'in ke nan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, manufar da tsohon shugaban kasar Sin Deng Xiaoping ya kirkiro, yayin cikakken zama na uku na kwamitin koli na 11 wanda ya gudana a shekarar 1978.
Shekaru 40 bayan aiwatar da wannan manufa, ta sanya kasar Sin a taswirar duniya a fannonin ci gaban kimiya da fasaha da zirga-zirgar sararin samaniya da fannin kirkire-kirkire.
A kwanakin baya ne, aka shirya wani nune-nune game da ci gaban da kasar Sin ta samu a fannonin daban-daban shekaru 40 bayan aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje.
Nune-nunen sun hada da ci gaban kimiyya da fasaha, kirkire-kirkire, fasahar masana'antu, fasahar mutun-mutumi, fasahar tauraron dan adam, noma na zamani, kiyaye muhalli, na'urorin kiwon lafiya, kayan aikin soji, na'urorin motsa jiki, da dai sauransu. Nasarar kasar Sin a fannin yaki da talauci da kirkire-kirkirkire da fannin tauraron dan adam a fannoni da dama, da suka hada na hasashen yanayi, ingacin iskar da ake shaka, da gudanar da bincike da tattara bayanan kan teku da tsibbirai da sadarwa da dai sauransu. An nuna irin ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin kera jiragen kasa masu saurin tafiya da jirgin sama samfurin C919 wanda kasar Sin ta kera da kanta. Mahalarta taron ya kunshi 'yan jaridu daga sassa daban daban na gidan radiyon kasar Sin da sauran kafafen yada labarai da jaridu na gida da na ketare, da kuma manyan jami'an ofisoshin jakadancin kasashe daban daban dake aikin a kasar Sin. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)