181120-baki-sama-da-dubu-sun-halarci-bikin-baje-kolin-sauye-sauyen-da-suka-faru-a-sakamakon-yin-gyare-gyare-da-bude-kofa-cikin-shekaru-40-da-suka-wuce-luba.m4a
|
A jiya Litinin a nan birnin Beijing, baki sama da dubu da suka hada da jami'an diplomasiyya, da kwararru, da kuma jami'an hukumomin kasuwanci na kasashe daban daban da ke nan kasar Sin sun halarci bikin baje kolin sauye-sauyen da suka faru, sakamakon manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje.
Bikin na da jigon "Gaggaruman sauye-sauye, murnar cika shekaru 40 da aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje", kuma baki mahalarta bikin sun bayyana cewa, cikin shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin ta samu ci gaban a zo a gani da ya burge kasashen duniya, kuma suna fatan inganta hadin gwiwarsu da kasar Sin don cimma moriyar juna.
A wajen bikin, sakatare na daya daga ofishin jakadancin kasar Pakistan da ke kasar Sin, Raheel Tariq ya kwaikwayi yadda aka tuka jirgin kasa mai saurin gaske wanda ake kira Fuxing a samfurin jirgin da aka samar, kuma ya bayyana cewa, ci gaban da kasar Sin ta samu ta fannin zirga-zirga da tattalin arziki na zamani, da kuma fasahohin yanar gizo sun fi burge shi, ya ce, "Na yi farin cikin ganin yadda kasar Sin ke saurin ci gaba, da kuma yadda tattalin arzikin kasar Sin ke bunkasa, gaskiya abun mamaki ne. Kasar Pakistan na iya koyon fasahohin ci gaba da yawa daga gare ta, kuma ina fatan kasashen biyu za su iya hadin gwiwa da juna bisa karin fannoni, a yunkurin cimma moriyar juna."
Abubuwan da aka baje kolinsu sun hada da mutum-mutumin da suka alamanta fara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, da jerin rokoki samfurin Changzheng na daukar kumbuna, da kuma samfurin tashar sararin samaniya ta Tiangong da sauransu, sauye-sauyen da suka faru a kasar Sin a sakamakon manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje ba kawai sun jawo hankalin duniya ba, hatta ma suna ta kara amfana wa al'ummar kasashen duniya bisa manufar kyakkyawar makoma ta bai daya ga dukkanin bil Adam.
Chenoa, sakatariya ta daya daga ofishin jakadancin kasar Uruguay ta ce, manufar yin gyare-gyare da bude kofa na da muhimmiyar ma'ana ga kasar Sin, kuma tana cike da imani ga ci gaban kasar Sin, ta ce, "A ganina, wannan biki biki ne mai kasaita, kuma muna bukatar kara fahimtar tarihin kasar Sin, da kuma nasarorin da kasar Sin ta cimma. Ci gaban kasar Sin ya jawo hankalin duniya, musamman ma ci gabanta ta fannin kimiyya da kirkire-kirkire ya fi burge ni."
Ta hotuna da bayanai da hoton bidiyo da samfura da sauransu ne, bikin ya nuna sauye-sauyen rayuwar al'ummar kasar Sin cikin shekaru 40 da suka wuce, musamman ma tun bayan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar karo na 18 da aka kira a shekarar 2012. (Lubabatu)