in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Ana inganta hadin kan kasashen Asiya da Tekun Fasifik bisa ka'idojin "bude kofa, kirkir-kirkire, da hakuri da juna"
2018-11-18 21:37:45 cri

A ranar Lahadi 18 ga wata, aka rufe kwarya-kwaryan taro karo na 26 na shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin kan kasashen da ke yankin Asiya da tekun Fasifik ta fuskar tattalin arziki wato APEC a kasar Papua New Guinea, wanda aka shafe kwanki biyu ana yinsa. A yayin taron mai taken "yin amfani da damammaki bisa tushen yin hakuri da juna domin gina kyakkyawar makoma ta zamani", kasashe mambobin kungiyar sun cimma daidaito a fannonin kara cudanya da juna, da raya yankin ciniki maras shinge a yankin Asiya da tekun Fasifik, da raya tattalin arziki na salon zamani, da ma sabon buri, bayan cimma Burin Bogor, sa'an nan sun bayyana matsayinsu na bai daya na goyon baya da kiyaye tsarin ciniki cikin 'yanci da ke tsakanin bangarori daban daban, da ma dunkulewar tattalin arzikin duniya wuri daya.

Abin da ya kamata a lura shi ne, sassa daban daban sun amince sosai kan matakai biyar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar bisa ka'idojin "bude kofa, neman bunkasuwa, hakuri da juna, kirkire-kirkire da ma bin ka'ida". Ana hasashen cewa, wannan shirin da kasar Sin ta tsara zai karfafa hadin gwiwar kasashen Asiya da tekun Fasifik a fannoni uku.

Na farko, bude kofa ga waje zai sa kaimi ga samun kyakkyawar makomar kasashen da ke Asiya da tekun Fasifik.

Yanzu yankin da kasashen ke ciki ya samu damammaki sakamakon dunkulewar tattalin arzikin duniya wuri daya, da juyin juya hali da ake yi kan fasahohi da masana'antu. Amma a sa'i daya kuma, matsalar kin yarda da dunkulewar duniya wuri daya da ma rikicin cinikayya tana ta tsananta, akwai rashin tabbas sosai wajen samun bunkasuwa. A yayin taron, Shugaba Xi ya yi kira ga kasashe daban daban da su kokarta wajen raya tattalin arziki mai salon bude kofa, da ci gaba da sa kaimi ga samar da 'yanci da saukaka cinikayya da aikin zuba jari, bisa la'akari da yanayin ci gaban duniya da ake ciki, lamarin da zai ba da hanya ga raya makomar yankin.

Idan mun dauki kasar Sin a matsayin misali, a yayin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin da aka rufe ba da jimawa ba, jimillar ciniki da aka yi tsakanin bangarori daban daban ta kai dala biliyan 57.8, wanda ya sa aka ga alfanun da aka samu sakamakon bude kasuwarta da Sin ta yi, haka kuma ake gane cewa, rufe kofa ba shi da makoma. Sabo da haka ne ma, a yayin taron na APEC, shugabanni kasashe mahalarta taron suka bayyana cewa, za su goyi bayan tsarin ciniki tsakanin bangarori daban daban, da goyon bayan rawar da WTO ke takawa. Muddin aka dauki wannan ra'rayi na bai daya, za a iya tabbatar da ci gaban yankin yadda ya kamata.

Na biyu, muhimmin aiki na hadin gwiwar kasashen Asiya da tekun Pasifik shi ne yin kirkire-kirkire.

A halin yanzu, tattalin arziki a fannin sadarwa ya kasance muhimmin karfi na yin kwaskwarima kan sha'anin duniya. A shekarun baya baya nan, membobin kungiyar APEC sun gabatar da manufofi da shirye-shiryen raya tattalin arziki a fannin sadarwa, don inganta wannan sha'ani cikin hanzari. Amma kashi 35 cikin dari na kasashe dake yankin kungiyar APEC suna fuskantar matsalolin yanayin raya tattalin arziki a fannonin sadarwa da fasahohi.

Tun da aka shigar da tattalin arziki a fannin yanar gizo karo na farko a cikin tsarin hadin gwiwa na kungiyar APEC a wurin taron koli na Beijing na kungiyar a shekarar 2014, kana aka tsara shirye-shiryen raya tattalin arziki a fannonin yanar gizo da sadarwa a taron koli na Da Nang na kungiyar a shekarar 2017, da kuma gabatar da taken "ana maraba da makoma mai amfani da fasahohin sadarwa", da kafa tsarin gwaji na kula da harkokin shige da fice ta yanar gizo na yankin Asiya da tekun Pasifik, da kuma kafa tsarin kula da karuwar cinikin dake tsakanin membobin kungiyar APEC da sauransu, wannan ya shaida cewa, tattalin arziki a fannin sadarwa ya zama sabon karfi na inganta kungiyar APEC a nan gaba.

Game da wannan, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, tattalin arziki a fannin sadarwa shi ne muhimmin aikin raya yankin Asiya da tekun Pasifik har ma ga dukkan duniya, ya ba da shawarar neman sabbin hanyoyin samun ci gaba, da kara gina ayyukan raya tattalin arziki a fannin sadarwa, da kuma kara samun moriyar da irin tattalin arzikin ya kawo da sauransu. Wannan ya shaida ra'ayin kasar Sin game da makomar tattalin arziki a fannin sadarwa, tare da fatan kasar Sin na more fasahohi a wannan fanni tare da kasashen Asiya da tekun Pasifik har ma dukkan kasashen duniya.

A hakika dai, a matsayin kasa mai ci gaban fasahohin sadarwa, kasar Sin ta yi kirkire-kirkire kan fasahohin raya tattalin arziki a kan yanar gizo da saye da sayarwa da kuma biyan kudi ta intanet, wanda ya samar da gudummawa wajen raya tattalin arziki a fannin sadarwa a yankin Asiya da tekun Pasifik. Alal misali, a kasar Papua New Guinea da aka gudanar da taron koli na kungiyar APEC a wannan karo, kamfanonin Sin sun taimakawa kasar wajen gina hanyoyin yanar gizo wadanda suka hada da jihohi 14 na kasar. Kana wakilai masu halartar taron sun bayyana amincewarsu ga tsarin raya ciniki ta yanar gizo na kasar Sin da fasahohin da Sin ta samu a wannan fanni. Shugaban taron manyan jami'an kungiyar APEC Ivan Pomaleu ya ce, a sakamakon bunkasuwar tattalin arziki a fannin yanar gizo ta kasar Sin, Sin ta taka muhimmiyar rawa a wannan fanni.

Na uku, ana bukatar yin hakuri da juna yayin da ake kokarin raya yankin Asiya da tekun Pasifik.

La'akari da bambance-bambance dake tsakanin kasashen yankin na Asiya da tekun Pasifik, idan ba su yi hakuri da juna ba, to zai wahala su samu ci gaba, duk da cewa kusan dukkan kasashen dake yankin suna son raya tattalin arziki irin na zamani, amma ana bukatar wasu sharudan da wasu kasashe ba su samu ba tukuna a halin da ake ciki yanzu, misali manyan kayayyakin more rayuwar jama'a na zamani da fasahohi na zamani da fitattun kwararrun da abin ya shafa da sauransu, a don haka batun yin amfani da damammakin samun ci gaba bisa tushen yin hakuri da juna ya fi jawo hankalin mahalartan taron.

A nasa bangare, shugaba Xi Jinping ya yi kira ga kasashe daban daban da su mai da hankali kan hakikanin yanayin da suke ciki, haka kuma su martaba juna, ta yadda za su samar da damammaki ga daukacin kasashen dake yankin, a karshe dai za su cimma burin tabbatar da dauwamammen ci gaba mai daidaito a yankin.

Yin cudanya tsakanin sassa daban daban tushe ne na samun ci gaba, kasar Sin ta riga ta ba da misali wajen gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya, a shekarar 2017, adadin cinikin dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashen da suka shiga shawarar ya kai dalar Amurka biliyan 1440 da miliyan 320, a sa'i daya kuma, an samar da guraben aikin yi da yawansu ya kai dubu 244 a wuraren da ake aiwatar da shawarar. A cikin jawabinsa, shugaba Xi ya bayyana cewa, bayan kokarin da ake yi cikin shekaru biyar da suka gabata, ya zuwa yanzu shawarar ziri daya da hanya daya ta riga ta shiga wani sabon mataki, firayin ministan kasar Canada wanda ya haharci taron Justin Trudeau shi ma ya bayyana cewa, gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a a fadin duniya yana samar da sabbin kasuwanni da sabbin albarkatu da sabbin damammakin samun ci gaba ga kasashe daban daban a fadin duniya.

Yanzu an riga an kawo karshen taron kolin kasashe mambobin kungiyar APEC a kasar Papua New Guinea, yankin nan na Asiya da tekun Pasifik zai samu sabon ci gaba karkashin kokarin da kasashen suke yi, yanzu aiki mafi muhimmanci shi ne tsara wani sabon shiri a maimakon shirin Bogor da aka tsara a garin Bogor na kasar Indonnesiya a shekarar 1994. Dangane da wannan, kasar Sin ta gabatar da ra'ayinta a fannoni uku da suka hada da kafa yankin ciniki maras shinge, da cudanya tsakanin kasashe daban daban dake yankin da kuma raya tattalin arziki irin na zamani bisa tushen yin hakuri da juna, manufar da za ta sa kaimi kan ci gaba a yankin. Amma yanzu yanayin da tattalin arzikin duniya ke ciki na fuskantar manyan sauye-sauye, bunkasuwar tattalin arziki a yankin Asiya da tekun Pasifik ita ma ta gamu da matsaloli, a don haka dole ne kasashen dake yankin su aiwatar da manufar bude kofa da kirkire-kirkire da yin hakuri da juna, haka kuma su daidaita sabanin dake tsakaninsu, tare kuma da shawo kan kalubalen dake gabansu, ta yadda za su gina kyakkyawar makoma a yankin yadda ya kamata.(Kande Zainab Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China