in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu sauyi game da dangantakar Sin da Australia
2018-11-16 20:20:12 cri
Kwanan nan, kasar Australia ta yi ta nuna zumunci ga kasar Sin. A yayin taron koli na ASEAN da aka gudanar a kwanan baya, sabon firaministan kasar Scott Morrison ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Sin Li Keqiang, wanda ya kasance muhimmiyar alama, ta kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, tun bayan da suka samu tabarbarewar ta.

Ko da yaushe kasar Sin na dora muhimmanci, da kuma kiyaye dangantakar dake tsakaninta da Australia, tana kuma mai da gwamnatin Morrison da ta soma rike ragamar mulkin kasar a watan Agusta, a matsayin wata dama mai kyau, ta kyautatta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, tare kuma da ba da tabbaci kan ra'ayi mai yakini da kasar Australia ta nuna kan dangantakarsu.

Game da mua'ammala mai kyau da ake yi tsakanin Sin da Australia a kwanan nan, ya kamata Australia ta martaba kyakkyawan matsayin da Sin ke dauka, ta kuma yi kokari wajen bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata a cikin dogon lokaci, a maimkon la'akari da wasu dalilan siyasa a cikin kasar.

Ba za a manta ba, a cikin shekara daya da rabi da suka gabata, manufar da kasar Australia ta dauka kan kasar Sin na cike da kiyayya, wanda hakan ya lalata tushen siyasa, da na ra'ayin jama'a ta fuskar hadin kai ta sada zumunci a tsakanin kasashen biyu. Ga misali, kasar Australia ta jagoranci kasashen yamma, wajen yayata ra'ayin wai "kasar Sin na tsoma baki cikin harkokin gidan wasu sassa", da kuma tsara wata doka domin nuna adawa da kasar Sin bisa zargin "tsoma baki cikin gida na wasu kasashen ketare".

Kasar Austrlia da ta kasance "Jagora kuma uwa ta adawa da kasar Sin" ta sanya an samu tabarbarewar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Manazarta sun yi nuni da cewa, ta yin la'akari da babban zaben da za a gudanar a shekara mai zuwa, gwamnatin kasar Australia na damuwa da illolin da ka iya shafar tattalin arzikin kasar, a sakamakon tabarbarewar dangantakar da ke tsakaninta da kasar Sin, wadda ta kasance abokiyar ciniki mafi girma a gare ta, don haka ya zama wajibi ta kyautata dangantakarta da kasar Sin.

A kwanan baya ne, tsohon ministan harkokin waje na kasar Australia Alexander Downer ya bayyana cewa,"Damuwar da aka bayyana game da bunkasuwar kasar Sin ba shi da tushe, kuma za mu yi shirme idan muka dauki manufar yunkurin dakile kasar Sin".

A farkon watan nan da muke ciki, ministar harkokin waje na kasar Australia Marise Payne ta kawo ziyara nan kasar Sin, inda ta kuma gana da darektan hukumar hadin gwiwar samar da ci gaban kasa da kasa ta kasar Sin, wadda ba ta jima da kafuwa ba. A wata mai zuwa kuma, tsohon firaministan kasar John Howard, zai kawo ziyara nan kasar don halartar wani babban taro na shawarwari.

Tuni dai firaministan kasar Australia Scott Morrison ya bayyana cewa, bunkasuwar kasar Sin, dama ce da ake fuskanta a maimakon barazana, kuma yana son inganta huldar abokantaka da ke tsakanin kasashen biyu daga dukkanin fannoni. Muna kuma fatan ba saboda zabe ne gwamnatin Australia ta yi wannan zabi ba, sai dai domin hangen nesa game da bunkasa dangantaka da ke tsakanin kasashen biyu.(Bilkisu Xin, Lubabatu Lei)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China