in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin a Najeriya ya tabo magana kan CIIE
2018-11-13 13:16:21 cri

Jaridar Daily Trust ta tarayyar Najeriya ta ruwaito wani rahoto a ranar 10 ga wata, bayan zantawar wakilinta da jakadan kasar Sin a kasar, Zhou Pingjian, kan batutuwan da suka shafi matakan da aka dauka bayan kammala taron kolin Beijing na dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin daga ketare wato CIIE karo na farko da aka yi a birnin Shanghai, da kuma huldar abota dake tsakanin Sin da Najeriya da sauransu.

Game da matakan da aka dauka bayan kammala taron kolin Beijing na dandalin hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, jakada Zhou Pingjian ya bayyana cewa, taron kolin Beijing na bana, wani gagarumin taro ne dake kunshi da tarihi. Bisa matsayinta na babbar kasa a nahiyar Afirka, tarayyar Najeriya ta ba da gudummowarta kan gudanar da taron cikin nasara, kuma gwamnatin kasar Sin ta yaba da kokarin da ta yi matuka.

A ranar 5 ga watan Satumban da ya gabata, wato bayan kammala taron koli a birnin Beijing, nan take shugaban kasar Sin Xi Jinping da firayin minstan kasar Li Keqiang, suka gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ya zama shugaban Afirka na farko da shugabannin kasar Sin suka gana da shi bayan rufe taron. Yayin ganawar tasu, shugabannin kasashen biyu sun tattauna kuma sun yi musanyar ra'ayoyi masu zurfi kan batutuwan dake shafar yadda za su aiwatar da sakamakon da aka samu yayin taron, da kuma yadda za su kara zurfafa huldar dake tsakanin kasashensu, haka kuma sassan biyu sun cimma matsaya guda kan su.

Daga baya mai taimakawa ministan harkokin wajen kasar Sin Chen Xiaodong, ya kai ziyara Najeriya a karshen watan Oktoban da ya wuce, inda ya yi shawarwari da mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo, da ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyeama, da kuma ministar harkokin gida na kasar, ziyarar da ta sa kaimi ga hadin gwiwar dake tsakanin sassan matuka.

Yayin taron kolin Beijing, shugaba Xi ya sanar da manyan shirye-shirye guda takwas da kasar Sin za ta aiwatar a kasashen Afirka domin taimaka musu, wadanda ke kumshe da raya masana'atu, da gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, da saukaka ayyukan gudanar da cinikayya tsakanin sassan biyu, da samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da sauransu. Wakilin jaridar ya yi wa jakada Zhou tambaya, kan bangaren dake cikin wadannan shirye-shirye takwas da Najeriya za ta fi samun moriya.

Inda Jakada Zhou ya bayyana cewa, bayan taron kolin Beijing, gwamnatin kasar Sin ta samar da kudin da yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 60 domin aiwatar da wadannan shirye-shirye takwas, kuma yana sa ran gwamnatin Najeriya za ta yi nazari kan su saboda duk wadannan suna shafar babbar moriyar al'ummar kasar, daga baya kuma ya dace gwamnatocin kasashen nan biyu wato Sin da Najeriya su kara karfafa cudanyar dake tsakaninsu, ta yadda za su gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu lami lafiya.

Kamar yadda aka sani, kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, Najeriya ita ma kasa ce mai tasowa mafi girma a nahiyar Afirka, a don haka kamata ya yi kasashen biyu su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu bisa tushen daidaito, musamman ma fannonin gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a da aikin gona da samar da kayayyakin masana'antu da cudanyar al'adu domin samun moriyar juna.

Game da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin daga ketare wato CIIE karo na farko da aka gudanar a birnin Shanghai tsakanin ranekun 5 zuwa 10 ga wata, jakada Zhou Pingjian ya bayyana cewa, makasudin shirya irin wannan gagarumin bikin kasa da kasa a kasar Sin shi ne, kara bude kofa ga kasashen duniya, kamar yadda shugaba Xi ya jaddada cewa, bude kofa zai samar da ci gaba, yayin da rufe kofa zai jawo koma baya, a don haka kasar Sin za ta kara bude kasuwarta ga daukacin kasashen duniya, haka kuma ya nuna cewa, kasar Sin tana nacewa ga manufar gudanar da cinikayya tsakanin bangarori daban daban, kuma tana yin kokari domin raya cinikayya maras shinge, tare kuma da kara habaka cudanyar tattalin arziki a fadin duniya.

Jakada Zhou ya kara da cewa, CIIE zai samar da wani sabon dandali ga kasuwar kasar Sin da kasuwar duniya, yana mai fatan 'yan kasuwar Najeriya za su samu sabbin damammaki daga bikin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China