in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin Ta Shiga Zamanin Karuwar Matsayin Sayayya
2018-11-12 21:06:01 cri
Jimillar kudaden cinikayyar da aka kulla, sakamakon bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su nan kasar Sin irin sa na farko da ya kammala ranar Asabar a birnin Shanghai na CIIE, sun kai dala biliyan 57.83, kana kudaden kayayyakin da aka sayar a ranar rangwame ta kasar sun kai dala biliyan 30.7. Wannan karfin sayayya ya nuna cewa, kasar Sin na da makoma mai kyau a fannin hada hadar sayayya, ta kuma shiga zamani na karuwar matsayin sayayya mai inganci.

Alibaba, babban kamfanin cinikayya ne ta intanet, ya kaddamar da garabasar sayayyarsa a ranar 11 ga watan Nuwamban 2009, ranar da matasan Sinawa ke daukarta a matsayin bikin gwagware, a sakamakon yadda ta yi kama da sanduna 4 dake alamta gwauro da Sinanci.

Bayan ci gaba da bunkasa garabasar a cikin shekaru 10 da suka gabata, yanzu ta riga ta kasance bikin sayayya mafi girma a duk duniya, kuma an mai da ita a matsayin hasashen kasuwar sayayya ta kasar Sin.

Idan aka kwatanta wannan shekara da shekarun baya, za a gane cewa, sayayyar ranar gwagware ta sha bamban a wannan shekara, wato ta zo ne daf da kammalar bikin baje kolin kayayyakin kasa da kasa da ake shigo da su kasar Sin, wanda aka kammala shi a ranar Asabar da ta gabata, bikin da ya samu halartar sama da 'yan kasuwa dubu 400 daga gida da kuma waje, don haka, an kara samun kayayyakin na kasashen ketare a sayayyar ranar gwagware ta wannan shekara.

Misali, kamfanin Tmall da ke sayar da kayayyaki ta yanar gizo, a wannan shekara ya tallata kayayyakin samfura kusan dubu 20 da suka zo daga kasashe da shiyyoyi 75. Amfanin gona masu inganci da suka hada da 'ya'yan itatuwan nan da ake kira avocado na kasar Mexico, da jan jatanlanle na kasar Argentina, da kuma kifin Salmon na kasar Denmark sun samu matukar karbuwa. Har wa yau, na'urorin zamani da suka hada da mutum-mutumin inji da ke iya tsabtace daki, da makulli na zamani ma an sayar da su da yawan gaske. "Sayen kayakin kasashen duniya ba tare da zuwa kasashen ba" sun riga sun zama salon rayuwar Sinawa.

Irin wannan yanayi, watakila ko mutanen da suka tsara bikin sayayyar ranar gwagware ma ba su taba tsammani ba. Daga shekara ta 2009 zuwa ta 2018, yawan kudin cinikin sayayyar ranar gwagware ya karu daga kudin Sin Yuan miliyan 50 zuwa Yuan biliyan 213.5, kana kuma yawan kamfanonin da suka halarci wannan biki ya karu daga guda 27 kawai zuwa sama da dubu 180. Irin canje-canjen da aka samu a yayin bikin sayayyar ranar gwagware a cikin shekaru goma da suka wuce, sun nuna sauye-sauyen harkokin saye da sayarwa na al'ummar kasar Sin, kuma sun nuna cewa tattalin arzikin kasar Sin na bunkasa ta hanyar da ta dace, kana al'ummar kasar na da imanin sosai ga makomar tattalin arzikin kasar.

Alkaluman da aka bayar sun bayyana cewa, daga watan Janairu zuwa Satumbar bana, yawan kudin saye da sayarwa da al'ummar kasar Sin suka kashe, ya bayar da gudummawar kashi 78 bisa dari na bunkasuwar tattalin arzikin kasar, wanda ya karu da kashi 14 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. A halin yanzu harkokin saye da sayarwa suna bada babban taimako ga ci gaban tattalin arzikin kasar Sin. Nan da shekaru 15 masu zuwa, an yi hasashen cewa, kasar Sin za ta shigo da kayayyaki daga kasashen waje, wadanda darajarsu za ta kai dala triliyan 30, a wani kokari na biyan bukatun jama'a na zaman rayuwar yau da kullum. Ko shakka babu, kasar Sin ta ci gaba da zama babban karfi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya.

(Masu fassara: Bilkisu Xin, Lubabatu Lei, Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China