181120-Tattaunawa-da-Tijjani-Inuwa-Babura-jamiin-maaikatar-masanaantu-da-cinikayya-da-zuba-jari-ta-Najeriya.m4a
|
A yayin da ake gudanar da wannan biki, wato ranar 8 ga watan Nuwamba, tawagar ma'aikatar masana'antu da cinikayya da zuba jari ta Najeriya da ta zo birnin Shanghai ta hada kai da karamin ofishin jakadancin Najeriya dake Shanghai, don shirya wani dandalin tattaunawa kan harkokin cinikayya da zuba jari, wato Nigeria Trade and Investment Forum 2018. Dandalin ya samu halartar jami'ai daga ma'aikatar masana'antu da cinikayya da zuba jari ta Najeriya, da jami'an diflomasiyyar Najeriya dake Beijing da Shanghai da Guangzhou da Hong Kong, da 'yan kasuwa da kamfanonin Najeriya dake kasar Sin, tare kuma da takwarorinsu na kasar Sin wadanda ke da niyyar zuba jari a Najeriya.
A nasa bangaren, babban sakataren ma'aikatar masana'antu da cinikayya da zuba jari ta Najeriya, Mista Sunday Edet Akpan ya bayyana cewa, Najeriya na da kyakkyawan yanayin zuba jari da gudanar da kasuwanci, inda ya yi maraba da 'yan kasuwa da kamfanonin kasar Sin da su je Najeriyar don su zuba jari.
A wajen dandalin tattaunawar, wakilinmu Murtala Zhang ya samu damar zantawa da daya daga cikin membobin tawagar ma'aikatar masana'antu da cinikayya da zuba jari ta Najeriya wadanda suka zo birnin Shanghai, wato Malam Tijjani Inuwa Babura, darekta mai kula da manufofi da tsare-tsare da bincike gami da yin kididdiga a ma'aikatar, inda ya bayyana makasudin ziyararsu Shanghai, da yadda ma'aikatarsu take kokarin bunkasa harkokin cinikayya da zuba jari tsakanin Sin da Najeriya.
Ga yadda tattaunawar tasu ta kasance.