in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya za su dade suna amfana da bikin baje kolin CIIE
2018-11-11 20:30:49 cri
A jiya Asabar aka rufe bikin baje kolin kasa da kasa na farko na kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin wato CIIE a takaice, a birnin Shanghai na kasar. A cikin kwanakin shida da suka wuce, kasashe da shiyyoyi da kuma kungiyoyin kasa da kasa 172 ne suka halarci bikin, a yayin da kamfanoni sama da 3600 suka baje kolin kayayyakinsu, kuma masu sayayya sama da dubu 400 da suka zo daga cikin gida da kuma waje sun yi shawarwari tare da masu baje kolin, wadanda suka yanke shawarar kulla cinikayya da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 57.83, nasarar da ba a taba ganin irinta ba a tarihi, don haka ne kuma 'yan kasuwa da suka baje kolin kayayyakinsu da yawa sun ce ba su so su yi ban kwana da bikin ba, kuma za su sake zuwa a shekara mai zuwa.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ne ya sanar da shirya bikin baje kolin a yayin taron kolin hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar ziri daya da hanya daya da ya gudana a bara, kuma bikin ya kasance wani muhimmin matakin da kasar ta dauka a kokarin kara bude kofarta ga kasashen waje. Nasarorin da aka cimma a yayin bikin sun kuma shaida cewa, "dunkulewar tattalin arzikin duniya shi ne kokarin da ake yi a duniya, wanda ba za a iya canza shi ba", kuma "bude kofa da hadin gwiwa su ne ke samar da kuzari ga harkokin ciniki na duniya". Bikin na wannan karo zai amfana wa kasashen duniya cikin wani lokaci mai tsawo.

Na farko dai, bikin ya taimaka wajen bude kofar kasashen duniya, kuma ya taimaka ga samar da 'yancin yin ciniki da bunkasuwar tattalin arzikin duniya. A yayin da ake fuskantar ra'ayi na nuna kyamar dunkulewar tattalin arzikin duniya da kuma kariyar ciniki, asusun ba da lamuni na duniya wato IMF ya daidaita hasashen karuwar tattalin arzikin duniya cikin wannan shekara da kuma shekara mai zuwa daga kaso 3.9% zuwa 3.7%, matakin kuma da ya jawo damuwar kasa da kasa. A daidai wannan lokaci kuma, kasar Sin ta shirya bikin baje kolin kayayyakin kasa da kasa da ake shigo da su kasar, wanda ta sa masa taken "sabon zamani kuma makoma ta bai daya", don biyan bukatun kasa da kasa, tare da samar da wani dandali na bude kofa da hadin gwiwa da juna.

Na biyu, bikin CIIE ya sanya kasashen duniya tattara ra'ayin bai daya kan wasu manyan batutuwa game da tattalin arziki da cinikayya. Ba kamar sauran bukukuwan baje koli na shigi da fici ba, a yayin bikin CIIE na farko, baya ga baje koli, an kuma shirya taron dandalin tattaunawa kan manyan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya na duniya. Irin cudanyar tunani ta sanya bikin ya kasance wani sabon muhimmin dandamali wajen tattara ra'ayin bai daya na kasashen duniya, zai kuma amfanawa duniya martaba tsarin ra'ayin bai daya kan batutuwan.

Abin da ya fi muhimmanci shi ne, a yayin bikin CIIE an nuna ra'ayin yin shawarwari tare kan manyan manufofi, da kafa dandali tare, da kuma more nasarorin da aka cimma tare, hakan ya kasance aiwatar da manufar kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama. A yayin bikin, kasashe masu ci gaba sun kawo wasu fasahohi da kayayyaki na zamani, kasashe masu tasowa da wadanda ke fama da talauci sun nuna kayayyakinsu na abinci da amfanin gona, da tuffafi da kuma kayayyakin zaman rayuwar yau da kullum da suka kware a kai, dukkansu sun samu damar yin cinikayya da shigar da kayayyakin kasuwanni. Game da haka, babban daraktan kungiyar WTO Roberto Azevêdo ya ce, "Wannan wani gagarumin biki ne dake iya samar da moriya ga duk duniya, ciki har da kasashe masu tasowa da kasashen da suka ci gaba."

Bisa shirin da aka tsara, za a ci gaba da shirya bikin CIIE a ko wace shekara, ya zuwa yanzu akwai kamfanoni sama da 200 da suka sanya hannu kan yarjejeniyar halartar bikin karo na biyu. Wannan ya nuna cewa, bikin CIIE ya samu amincewa da karbuwa a duniya baki daya. (Masu Fassara:Lubabatu Lei Bilkisu Xin)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China