A cewar kamfanin Alibaba, mamallakin shagon TMall, sama da samfura 19,000 daga kasashe da yankuna 75 ne suka shiga aka dama da su ranar garabasar ta bana
Alibaba, babban kamfanin cinikayya ta intanet, ya kaddamar da garabasar sayayyar ce a ranar 11 ga watan Nuwamba 2009, ranar da matasan Sinawa ke daukarta a matsayin bikin gwagware. An zabi ranar ne saboda ranar ta 11 ga watan11, ta yi kama da sanduna 4 dake alamta gwauro da Sinanci.
Sayayyar farko da aka yi a shagon TMall, ta kai kimanin yuan miliyan 52. Jimilar cinikin da kamfanin ya yi a bakin dayan ranar a bara, ya kai yuan biliyan 168.2. (Fa'iza Mustapha)