in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan kasuwan Najeriya na son kara yin mu'amala da hadin-gwiwa da takwarorinsu na kasar Sin
2018-11-09 10:30:42 cri


Bikin baje-kolin kayayyakin kasa da kasa da ake shigowa da su kasar Sin karo na farko wanda ke gudana a birnin Shanghai a halin yanzu, wato CIIE a takaice, na samun halartar 'yan kasuwa da kamfanoni sama da 3600 daga yankuna da kasashe daban-daban na fadin duniya. Wasu 'yan kasuwan tarayyar Najeriya da suke halarci bikin, sun bayyana niyyarsu ta tallata kayayyakin kasar masu kyau zuwa ga kasar Sin, da kara samun fahimtar juna da mu'amala a tsakaninsu da 'yan kasuwan kasar Sin.

Efunnuga Martins Olanrewaju na daya daga cikin 'yan kasuwan Najeriya da suka zo birnin Shanghai don halartar bikin CIIE a wannan karo. Ya bayyana cewa, kofar kasar Sin a bude take don maraba da zuwan 'yan kasuwa da kamfanonin kasashe daban-daban na kasar, kana kuma kayayyakin kasashen waje suna iya samun damar shigowa kasuwar kasar Sin, al'amarin da ya burge shi kwarai da gaske. Mista Martins ya ce:"Shirya bikin CIIE wani muhimmin mataki ne da gwamnatin kasar Sin ta dauka don bude kasuwarta ga duk fadin duniya. A wannan karo mun kawo wasu kayayyaki kirar Najeriya masu kyau zuwa kasar Sin, ciki har da wani nau'in yadin gargajiya mai suna Adire, da sabulun wanka mai suna Dudu-Osun. A matsayina na dan kasuwan dake cinikin tufafi, abun da ya fi burge ni a nan kasar Sin shi ne, yadda Sinawa ke mutuntawa gami da rungumar al'adun gargajiyarsu, alal misali, na ga tufafin Sinawa na kunshe da al'adunsu iri-iri, wanda ya sa na karu sosai. Ko shakka babu, halartar bikin CIIE a wannan karo abu ne mai kyau gare ni."

"Adire" da Martins ya ambata, wani nau'in yadin gargajiya ne da ya samo asali daga birnin Abeokuta dake yankin kudu maso yammacin tarayyar Najeriya, wanda ke kunshe da al'adar rini ta tsawon shekaru sama da dari. A halin yanzu Adire yana samun karbuwa sosai a kasashe da dama dake yammacin Afirka. Wani dan kasuwan Najeriya na daban mai suna Nwozo Chimezie wanda ke halartar bikin CIIE a Shanghai ya bayyana cewa, akwai kamanceceniya da dama tsakanin al'adun Sin da Najeriya, abun da ya karfafa masa gwiwa sosai na cewa tufafin Adire za su samu karbuwa da amincewa a kasuwar nan ta kasar Sin. Mista Chimezie ya kuma ce, yana fatan ta hanyar halartar bikin CIIE, za'a kara nunawa al'ummar kasar Sin gami da sauran sassa duniya cewa, ban da albarkatun mai, Najeriya na da sauran kayayyaki masu kyau, inda ya ce:"Ba zan ce za mu iya daddale kwangiloli ko yin ciniki da yawa a wannan karo ba, ba haka nake fata ba. A halin yanzu a Najeriya, baya ga man fetur, koko da ridi su ne abubuwa biyu da muke fi fitarwa zuwa kasashen waje, amma ba mu maida hankali kan fitar da sauran kayakinmu ba, kuma mutane ba su sani ba. Muna so mu kulla zumunta da mu'amala da takwarorinmu na kasar Sin a Shanghai, da lalibo hanyar yin cinikayya tsakaninmu, saboda sanin kowa ne, kasar Sin ta fi kowace kasa yawan al'umma a duniya, kuma tana da babbar kasuwa, don haka na yi imanin cewa kayayyakinmu masu kyau kamar 'Adire' za su samu karbuwa a kasar Sin a nan gaba."

Baya ga 'yan kasuwan dake cinikin tufafi da kayan hannu, akwai sauran wasu 'yan kasuwan Najeriya wadanda suka zo birnin Shanghai don halartar bikin CIIE a wannan karo. Madam Chinyere Okpara-Adeniji ita ce babbar manajar wani kamfanin bayar da hidima ta fannin daukar ma'aikata a birnin Ikkon Najeriya. Ta bayyana cewa, bikin CIIE ya baiwa kamfanonin Afirka wata kyakkyawar dama ta shiga kasuwar kasar Sin, kuma tana fatan kamfaninta zai yi amfani da wannan dama don kulla zumunta da kamfanonin kasar Sin, da taimaka musu wajen zuba jari da gudanar da ayyuka a Najeriya, sa'annan a kara samar da guraban ayyukan yi a Najeriyar.

Madam Chinyere Okpara-Adeniji ta ce:"Makasudin zuwanmu birnin Shanghai a wannan karo shi ne neman kamfanonin kasar Sin wadanda ke da niyyar zuba jari a Najeriya, muna iya taimaka musu wajen gudanar da ciniki a Najeriya ba tare da wata matsala ba, har ma muna iya taimaka musu wajen daukar ma'aikata. A dayan bangaren kuma, muna kokarin neman damar kara samar da guraban ayyukan yi a kasarmu Najeriya, alal misali, idan wani kamfanin kasar Sin ya zo Najeriya, za mu bayyana musu wannan manufar, wato ya kamata su dauki ma'aikata 'yan kasar. Don haka idan muka yi hadin-gwiwa da kamfanonin kasar Sin, za mu dauko musu kwararrun ma'aikatan da suke bukata, da kuma samar da guraban ayyukan yi a Najeriya, al'amari ne da zai kawowa juna moriya."(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China