in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CIIE ya kara jaddada manufar kasar Sin na kara bude kofa ga kasashen waje
2018-11-08 12:03:15 cri

A ranar Litinin 5 ga watan Nuwamban shekarar 2018 ne, aka kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin na kasa da kasa CIIE karo na farko a brining Shanghai, inda kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa 172, tare da kamfanoni da masana'antu fiye da 3600 suka halarci wannan gagarumin bikin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa.

A jawabin da ya gabatar yayin bikin kaddamarwar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da ra'ayoyi uku na ingiza kasashen duniya da su kara yin hadin gwiwa da bude kofofinsu, ya kuma gabatar da matakai 5 da kasar Sin za ta dauka na kara bude kofarta ga daukacin duniya. Wadannan ra'ayoyi da matakai tamkar wani mataki ne na kokarin kare tsarin yin cinikayya maras shinge tsakanin bangarori daban daban, da bunkasa sabon tsarin tattalin arziki mai salon bude kofa, da kuma bunkasa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama da kasar Sin take yi a kullum.

Wadannan muhimman matakai biyar su ne, kara kokarin shigo da karin kayayyaki kasar Sin daga waje, kara saukaka matakan shigar baki 'yan kasuwa kasar Sin, samar da yanayin kasuwanci mafi inganci a duniya, sannan kara bude kofofin sabbin yankuna da fannoni ga waje, sai kuma ingiza kara yin hadin gwiwa tsakanin bangarori da dama ko tsakanin bangarori biyu.

Masu fashin baki na ganin cewa wadannan matakai 5 sun yi daidai da bukatu da fatan sauran kasashen duniya, kana matakan da kasar Sin za ta dauka zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin duniya bai daya da ma ci gaban tattalin arzikin duniya. Haka kuma bikin baje kolin na CIIE ya kara jaddada manufar kasar Sin na kara bude kofofi da ma kasuwanninta ga kasashen duniya, kana wata dama ce ga kasashen Afirka na tallata hajojinsu ga duniya. (Ahmed, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China