in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin Da Kasashen Duniya Na Bukatar Kafa Wata Gadar Neman Wadata Tare
2018-11-07 20:00:48 cri
Kwanan nan, ko shakka babu kasar Sin ta kasance daya daga cikin batutuwan da suka fi jawo hankulan kafofin watsa labaru na duniya baki daya.

A ranar 5 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi a yayin bikin baje kolin kasa da kasa karo na farko na kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin, inda ya ba da shawarar raya tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa irin na kirkire-kirkire da zai kunshi kowa da kowa, ya kuma sanar da cewa, kasarsa za ta dauki manyan matakai guda biyar don kara habaka bude kofa ga kasashen ketare, da kara karfin shigo da kayayyaki, da kuma kara sassauta ba da iznin shiga kasuwar kasar. Daga baya, a ranar 6 ga wata, an shirya taron tattaunawa tsakanin firaministan kasar Sin Li Keqiang da jami'an wasu manyan hukumomin kudi na kasa da kasa su 6, ciki har da bankin duniya, asusun IMF, kungiyar WTO da dai sauransu, inda aka tattauna yadda za a yi kokarin samun nasara tare a tsakanin tattalin arzikin kasar Sin da na duniya wajen hadin kai mai salon bude kofa, kana firaminista Li ya jaddada cewa, kasarsa za ta kara bude kofa ga kasashen ketare, da neman ci gaba mai inganci.

A wannan rana kuma, mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan ya bayyana a yayin dandalin tattaunawa kan tattalin arziki ta hanyar yin kirkire-kirkire, cewa kasar Sin za ta nace wajen gudanar da ayyukanta yadda ya kamata, da nacewa kan babbar manufarta ta bude kofa ga kasashen ketare, tare kuma da hada kai tare da kasashe daban daban don ciyar da dunkulewar tattalin arzikin duniya bai daya gaba mai salon kara bude kofa, hade da kowa da kowa, amfanawa kowa, zaman daidaito da kuma samun nasara tare.

A sa'i daya kuma, an shirya bikin baje kolin zirga-zirgar jiragen sama da kumbuna na kasa da kasa, da babban taron yanar gizo na kasa da kasa karo na 5 a nan kasar Sin daya bayan daya, hakan na nuna yadda kasar Sin take bayyana wa duniya aniyyarta ta neman ci gaba tare da sauran kasashen duniya ta hanyar hakikanan matakan da ta dauka na kara bude kasuwanninta ga duniya.

Kasar Sin na kokarin bude kofa da hada kai tare da kasashen duniya ne sakamakon manyan nasarorin da ta samu yayin aiwatar da manufar ta ta yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare shekaru 40 da suka gabata. A cikin wadannan shekaru 40, matsakaicin kudin shiga da Sinawa ke samu ya ninka sau 25, yawan kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasa wato GDP yana kuma ninkawa sau 1 a shekaru takwas takwas, Sinawa sama da miliyan 700 sun fita daga da talauci, wadanda yawansu ya kai kashi 70 cikin 100 a al'ummar da ke fama da talauci a duniya, ana iya cewa, kasar ta taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban duniya.

Yadda kasar Sin take bude kofarta, ba kawai ita kadai take samun ci gaban ba, har ma ta amfana wa duniya baki daya. A yayin da aka kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su nan kasar Sin, an gudanar da harkokin ciniki da kulla yarjejeniyoyi, a hakika, tattalin arzikin kasar Sin ya sauya daga mai fitar da kayayyakinta zuwa ketare zuwa ga harkokin sayayya.

Bana shekaru 10 ke nan da aukuwar rikicin kudi a duniya. A cikin wadannan shekaru 10 da suka wuce, kasashen duniya sun hada kansu don warware matsalolin da suke fuskanta, hakan ya sa tattalin arzikin kasar Sin ya fara farfadowa, duk da haka, akwai matsala da kalubale da ake fuskanta. Musamman ma a cikin shekaru biyu da suka wuce, an fuskanci tsarin ba da kariya ga harkokin ciniki da kuma takaddamar ciniki.

A irin wannan halin da ake ciki, matsayin da kasar Sin ta dauka da ma matakan da ta dauka na da matukar muhimmanci ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. A sa'i daya kuma, ya kamata kasa da kasa ma su hada gwiwa a fannonin manufofi, don fadada hanyoyin hadin gwiwa.

Duk da cewa kasar Sin ma na fuskantar wahala ta fannin ci gaban tattalin arzikinta a sakamakon karin rashin tabbas na tattalin arzikin duniya da kuma kariyar ciniki da tattalin arzikin duniya ke fuskanta, amma in an yi hangen nesa, za a ga cewa, tattalin arzikin kasar Sin na da kyakkyawar makoma. Kasar Sin ta yi alkawarin cewa, "kullum za ta kara kokari wajen bude kofarta ga duniya, tare da samar da kuzari ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, sa'an nan za ta zama babbar kasuwa ga kasashen duniya da kuma ba da gudummawarta wajen tafiyar da harkokin duniya", domin tabbatar da ganin kasashen duniya baki daya sun samu kyakkyawar makoma. Haka kuma kamata ya yi kasa da kasa su ma su rubanya kokarinsu, su kara kokarin bude kofofinsu don hada gwiwa da sauran kasashe, ta yadda za a tabbatar da ci gaban juna.(Masu fassara:Bilkisu Xin Lubabatu Lei, ma'aikatan sashen Hausa na CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China