in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar na fatan koyi daga kwarewar Sin a fannin raya tattalin arzikin wasanni da shirya gasar Olympics in ji wani jami'in kasar
2018-11-08 16:43:23 cri

Ministan ma'aikatar raya wasanni da matasa a kasar Masar Ashraf Sobhy, ya ce kasar sa na fatan koyi daga kwarewar Sin a fannin raya tattalin arziki a fannin wasanni, da shirya gasar Olympics.

Mr. Sobhy ya bayyana hakan ne, yayin zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua. Ya ce "A gani na Masar na da matukar sha'awar koyi daga kwarewar Sin, musamman a fannin raya wasanni, da tattalin arzikin wasanni. Jami'in ya bayyana hakan ne a gefen taron matasa na kasa da kasa da ya gudana a garin Sharm El-Sheikh na Masar, tsakanin ranekun 3 zuwa 6 ga watan nan, taron da ya samu halartar shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi.

Ministan ya kara da cewa, tuni kasar sa ta fara hadin gwiwa da Sin, ta yadda za ta samu damar aron fasahohin Sin a fannin tsara gasar Olympics, domin yin amfani da su a lokacin da za ta karbi bakuncin gasar.

A shekarar 2008 ne dai birnin Beijing ya karbi bakuncin gasar Olympics ta lokacin zafi, yanzu kuma shirye shirye sun yi nisa, game da shirin kasar Sin na karbar bakuncin gasar ta lokacin sanyi, wanda za a yi a shekarar 2022.

Wasu rahotanni daga Masar na cewa, kasar ta fara nazartar dabarun da za ta bi domin karbar bakuncin gasar Olympic ta shekarar 2032, tana kuma aiki tukuru, domin ganin ta cika dukkanin sharuddan da za a bukata, kafin ma ta mika bukatar yin hakan.

Mr. Sobhy ya ce, abun sha'awa game da Sin shi ne, yadda take maida hankali sosai game da harkokin matasan ta. Ya ce Sin na da shirye shirye da dama da za a iya koyi da su, ciki hadda wadanda suka jibanci yaki da talauci, da bunkasa kasuwanci da inganta salon jagorancin cinikayya, da kuma inganta kwarewar matasa.

"Mun gano cewa, muna da wuraren kamanceceniya da Sin, kuma muna da mahanga iri daya a game da abubuwa da yawa. Don haka muna aiki tare, don zakulo sassan kara hada gwiwa a fannin raya wasanni" A kalaman Mr. Sobhy.

A baya bayan nan, Mr. Sobhy ya zanta da tawagar matasan Sin, karkashin jagorancin shugaban gamayyar kungiyoyin matasan kasar Li Keyong, yayin taron matasan na kasa da kasa.

Ya ce na zanta da tawagar Sin dake halartar dandalin, game da yadda za mu iya kafa kawance kasashen biyu a fannin raya harkokin matasa. Sobhy ya kara da cewa, sassan biyu sun tattauna game da kafa wani mako na matasan kasashen biyu.

Karkashin hakan, akwai manufar bunkasa al'adu, da nune nunen wasanni, da musayar al'adu, da tattaunawa tsakanin matasan bangarorin biyu.

Ya ce ana sa ran sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin matasan sassan biyu a farkon shekarar 2019 dake tafe, kuma nan gaba kadan, tawagar Masar za ta ziyarci takwararta ta Sin domin kammala shirye shiryen hakan, da kuma tattaunawa game da dukkanin batutuwa masu nasaba da kudurin.

Game da taron dandalin matasan na kasa da kasa da ya gudana a kasar Masar kuwa, jami'in ya ce taron ya samu halartar matasa ya yawan su ya kai 5,000 daga kasashe kusan 160. Kaza lika taron ya nuna muhimmancin matasa a fannin gina rayuwar al'ummar yanzu, da ma al'ummun dake tafe nan gaba, yayin da Masar ke kallon matasa a matsayin tubulin gina yau da kuma goben ta.

Mr. Sobhy ya ce dandalin na da matukar muhimmanci wajen cimma bukatun bil Adama, da raya al'adu, da musayar basira, da yada bayanai, da cudanya tsakanin matasa daga kasashe da yankuna, da ra'ayoyi mabanbanta.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China